✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban Hukumar Leken Asirin Girka ya ajiye aiki

Ana zargin Hukumar Leken Asirin kasar ta yi kutse da wata manhaja mai suna Predator.

Shugaban Hukumar Leken Asirin kasar Girka, Panagiotis Kontoleon ya ajiye aiki kan zargin leken asirin wayar shugaban ‘yan adawar kasar.

Ofishin firayi ministan kasar, Kyariakos Mitsotakis, ne ya bayar da sanarwar ajiye aikin Kontoleon a ranar Juma’a.

Ajiye aikin shugaban hukumar leken asirin ya faru mako guda ne bayan da shugaban jami’iyyar adawar Nikos Androulakis ya shigar da koke Kotun Kolin kasar.

Shugaban adawar yana zargin Hukumar Leken Asirin kasar ta yi kutsen a wayarsa ne da wata manhaja mai suna Predator.

“Yan kwanki da suka wuce, Majalisar Tarayyar Turai ta sanar da ni cewa an yi kutse cikin wayata ta hanyar amfani da manhajar Predator” in ji Androulakis a hirarsa da ‘yan jarida.

Manhajar ta musamman, an kera ta ne domin yin kutse a cikin wayar hannu, a inda za ta kunna abin magana ko  kyamara ta wayar mutum domin leken asiri, ba tare da sanin mai wayar ba.

Majalisar Tarayyar Turai ta sa mambobinta a wani tsari na musamman da za a rika duba wayoyinsu domin gano ko ana bin diddiginsu ta waya ba bisa ka’ida ba.

Shugaban adawar ya kuma yi amfani da wannan tsari ne a watan Yuni a inda binciken farko ya nuna cewa an yi kutse cikin wayar ta sa.