✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Jamhuriyar Nijar ya lashe Kyautar Shugabancin Afirka

Shi ne mutum na bakwai da ta taba lashe kyautar.

Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar ya lashe lashe kyautar shekarar 2020 ta Dala ta Gidauniyar Mo Ibrahim na shugabancin Afirka.

Kwamitin bayar da kyaututtukan ya yaba wa shugabancin Shugaba Mahamadou Issoufou a Nijar, daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya.

Kwamitin ya ce, shguaban “ya inganta bunkasar tattalin arziki, ya nuna jajircewa wajen tabbatar da daidaito a yankin da kuma tsarin mulki, da kuma karfafa dimokiradiyyar Afirka.”

Shugaban ya yi wa’adi biyu na shekaru biyar a matsayin shugaban kasa daga 2011 wanda yanzu Tsohon Ministan Cikin Gida, wanda ya lashe zaben shugaban kasar a watan jiya, Mohamed Bazoum ne zai gaje shi.

Mista Issoufou wanda shi ne mutum na shida da ya samu lambar yabo ta Mo Ibrahim, ya wallafa ce kyautar ta karrama dukkan mutanen Nijar.

“Na dauki wannan lambar yabo a matsayin karfafa gwiwa don ci gaba da yin tunani da aiki a hanyar da za ta bunkasa kimar dimokiradiyya da kyakkyawan shugabanci, ba wai a Nijar kadai ba, har ma da Afirka da ma duniya baki daya.”

Sauran wadanda suka samu kyautar su ne:

  1. Tsohuwar Shugaban Liberia, Ellen Johnson Sirleaf ta Liberia (2017)
  2. Shugaba Hifikepunye Pohamba na Namibia (2014)
  3. Shugaba Pedro Pires na Cabo Verde (2011)
  4. Shugaba Festus Mogae na Botswana (2008)
  5. Shugaba Joaquim Chissano na Mozambique (2007).