✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban jam’iyyar PDP a Zamfara ya rasu

Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Mallaha Gusau ya rasu.

Shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Mallaha Gusau ya rasu.

Babban Daraktan Wayar da Kai da Watsa Labarai na fadar gwamnatin jihar, Yusuf Idris ne ya tabbatar wa da Aminiya hakan.

Ya ce marigayin mai shekaru 59 ya rasu ne a kasar Jamus bayan ya fama da ciwon koda wadda ake masa wankinta kafin liktoci su tabbatar da rasuwar tasa.

“Shekara 10 da suka shude, ya taba tafiya zuwa kasar Indiya saboda matsalar, amma a wannan karon sai ya yanke shawarar zuwa Jamus domin samun kulawa, a nan ne kuma Allah Ya karbi rayuwarsa”, inji Alhaji Yusuf.

Kafin rasuwarsa, marigayin ya taba rike mukamin Mataimakin Shugaban jam’iyyar ANPP da kuma shugabanta na riko lokacin mulkin tsoffin gwamnonin jihar, Ahmed Sani Yarima da Mahmud Aliyu Shinkafi.

Bayan komawar tsohon gwamna Shinkafin zuwa PDP ne marigayin ya bi shi daga ANPP inda ya zama shugabanta, daga bisani kuma ya sake zama shugabanta ana dab da zaben 2019 a jihar.

Ya rasu ya bar mata hudu da ’ya’ya da kuma jikoki.

Ana sa ran yin jana’izarsa da zarar gawarsa tai so Najeriya.