✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban karamar hukuma ya sauya sheka daga PDP zuwa APC a Sakkwato

Ana alakanta sauya shekar da hana shi takara da aka yi a PDP

Shugaban Karamar Hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato, Isah Salihu Bashir Kalanjeni, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP mai mulki a jihar zuwa jam’iyyar adawa ta APC.

A cikin daren Asabar ne Shugaban karamar hukumar ya sanar da daukar matakin a lokacin da ya tafi gidan jagoran jam’iyar APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

Shugaban karamar hukumar bai sanar da dalilinsa na ficewa a jam’iyyar ba, amma da yawan mutane na danganta hakan da hana masa tikitin takarar dan majalisar tarayya da zai wakilci mazabar Tangaza da Gudu, da yake zargin Gwamnan Jihar, Aminu Waziri Tambuwal da hana shi.

Magoya bayan jam’iyar PDP sun nuna takaicinsu kan matakin da Kalenjeni ya ɗauka in da suke danganta lamarin da Butulci saboda amintakar da ke tsakaninsa da Tambuwal.

Ciyaman din dai ya sauya shekar ne tare da shida daga cikin Kansilolin karamar hukumar su 10.

Wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na jam’iyar, Abdullahi Yusuf Hausawa, domin jin matsayar jam’iyyar PDP kan wannan sauyin shekar, amma bai daga wayar da aka kira shi ba.