✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Kasar Burundi ya rasu

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya rasu  yana da shekara 55 a duniya. Gwamnatin Burundi ta sanar da mutuwar Shugaba Pierre Nkurunziza bayan ya yi …

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya rasu  yana da shekara 55 a duniya.

Gwamnatin Burundi ta sanar da mutuwar Shugaba Pierre Nkurunziza bayan ya yi  fama da bugun zuciya a daren Talata talata, 9 ga watan Yuni.

Mutuwar ta Nkurunziza mai shekara 55 na zuwa ne bayan zaben kasar na watan jiya da dan takarar jam’iyyarsa Evariste Ndayishimiye ya samu gagarumin rinjaye wanda zai maye gurbinsa a watan Agusta.

Gwamnatin kasar ta ce a ranar Asabar an kwantar da shugaban gadon asibiti bayan ya fara jin alamun rashin lafiya.

Ya kuma  samu sauki daga baya amma sai a ranar Litinin ciwon bugun zuciya ya same shi, kuma kokarin da aka yi na ceto ransa ya faskara.