Shugaban Kasar Iran na farko, Abolhassan, ya rasu a Faransa | Aminiya

Shugaban Kasar Iran na farko, Abolhassan, ya rasu a Faransa

Shugaban Kasar Iran na farko, marigayi Abolhassan Banisadr
Shugaban Kasar Iran na farko, marigayi Abolhassan Banisadr
    Sani Ibrahim Paki

Shugaban Kasar Iran na farko bayan juyin-juya-halin 1979, Abolhassan Banisadr, ya rasu a birnin Paris na kasar Faransa inda ya jima yana rayuwa tun bayan guduwa daga kasarsa.

A cewar wata sanarwa da shafinsa na intanet da kuma rahotannin kafafen yada labaran kasar ta Iran, mai kimanin shera 88, tsohon Shugaban ya rasu ne bayan ya sha fama da doguwar jinya a a asibitin Salpêtrière da ke Paris.

An dai haife shi ne a shekarar 1933 a lardin Hamedan da ke Yammacin Iran, kuma da ne ga fitaccen malamin addini kuma aboki ga Ruhollah Khomeini, mutumin da ya jagoranci juyin-juya-halin da ya kai ga kawo karshen mulkin ‘Sha’ karkashin Mohammad Reza Pahlavi.

Abolhassan, wanda ya yi karatunsa a Turai dai tsohon mai adawa ne da salon mulkin sarauta na Sha a kasar, kuma daga bisani ya zama makusanci ga Khomeini, mutumin da ya taba sauka a Paris kafin zamansa Jagoran Addini na Iran daga bisani.

Zababben Shugaban Iran na Farko

Watanni kadan bayan juyin-juya-halin, Abolhassan ya zama zababben Shugaban Iran na farko a tarihi, bayan ya sami kuri’u masu yawa don yin mulkin shekara hudu.

Kazalika, jagoran addinin ya nada shi a matsayin mai rikon mukamin Babban Kwamnadan Askarawan kasar.

Shugaban dai ya yi fice ne wajen ajiye gashin baki da kuma sanya Kwat irin ta Turawa, sabanin dogayen riguna da rawanin da aka fi sanin masu juyin-juya-halin da su, ko da dai ra’ayinsu ya zo daya da nasu a kan akidar Shi’a.

Abolhassan dai ya fuskanci babban kalubale ne a lokacin mulkinsa lokacin da aka karbe iko da ofishin jakadancin Amurka da ke Tehran da rikice-rikicen da suka biyo bayansa, da kuma mamayar da kasar Iraq, karkashin mulkin marigayi Saddam Hussein ta yi wa kasarsa.

Hakan dai ya haifar masa da gagarumar matsala a mulkinsa, kuma ya tilasta masa arcewa ya bar kasar bayan kammala mulkinsa.

Marigayin dai ya shafe shekaru da dama yana rayuwa a kasar Faransa a karkashin kulawar ’yan sanda.

Ya kuma yi kaurin suna wajen sukar lamirin jagororin kasar ta Iran, sannan ya wallafa mujalla da littattafai da dama a lokacin rayuwarsa.