✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Kungiyar Malaman Musulunci ta Duniya ya rasu

Ya rasu yana da shekara 96 a duniya

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na kasar Masar, kuma Shugaban Kungiyar Malaman Addinin Musulunci ta Duniya, Sheikh Yusuf Al-Qaradawi, ya rasu.

An sanar da rasuwar tasa ce ranar Litinin a shafinsa na Twitter yana da shekara 96.

A baya dai malamin ya yi suna wajen gabatar da wani shiri mai suna “Shari’a da rayuwa” a gidan talabijin na Al-Jazeera.

Shirin dai na ba musulmi dama daga sassa daban-daban na duniya su bugo waya don ya ba su fatawoyi a kan abubuwan Musulunci iri-iri.

Malamin na cikin wadanda suka caccaki sojojin da suka yi wa zababben Shugaban Kasar Masar na farko, Mohammed Morsi, juyin mulki a 2013.

Sheikh Al-Qaradawi dai dan asalin kasar Masar da ke zaune a Qatar, kuma rasuwarsa ta jawo kaduwa daga Musulmai daban-daban a fadin duniya, musamman a kafafen sada zumunta na zamani.

Malamin dai ya wallafa littatafan Musulunci sama da 120 da kuma kasidu da makaloli sama da 60.