Shugaban Makarantar da aka sace a Kaduna ya kubuta | Aminiya

Shugaban Makarantar da aka sace a Kaduna ya kubuta

‘Yan bindiga
‘Yan bindiga
    Ahmed Ali da Rahima Shehu Dokaji

Shugaban Makarantar Nazarin Kididdiga ta Tarayya da ke Manchok a Jihar Kaduna, Mista Amos Magbon ya kubuta daga hannun ’yan bindiga bayan kwanaki biyu da sace shi.

An dai sace Mista Magbon ne a gidansa da ke Manchok a daren ranar Talata.

Wani dan uwansa da ya tabbatar da faruwar lamarin Innocent Magbon, ya ce ’yan bindigar sun sako Amos bayan awa 48 da sace shi, sai dai bai bayyana ko an biya kudin fansa ba gabanin sako shin.

Ita ma Brenda Friday, wacce ’ya ce ga wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) da ’yan bindigar suka kashe mahaifinta Philip Yatai, ta shaki iskar ’yanci a ranar Talatar.

Wakilin NAN din ne ya bayyana cewa ’yar tasa Brenda ta kubuta a daren ranar Talatar.