✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya ya rasu

Janar Ibrahim Atttahiru ya rasu a hatsarin jirgin sama.

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, ya rasu a hatsarin jirgin sama.

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta tabbatar cewa Janar Attahiru ya gamu da ajalinsa ne a hatsarin da jirginta ya yi a Kaduna.

“Jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ya yi hatsari a kusa da Filin Jirgin Sama na Kaduna, amma ba a kai ga gano abun da ya haddasa hatsarin jirgin ba tukuna,” inji sanarwar da kakakin Rundunar, Edward Gabkwet ya fitar.

Wata majiya ta ce mutum takwas ne a cikin jirgin da ya yi hatsari, wanda ake tunanin har da dogarinsa da wani Janar din soja da sauransu.

Laftanar Janar Attahiru, wanda dan asalin Jihar Kaduna ne, ya zama Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ne a ranar 26 ga Janairu, 2021.

Ya kammala Kwalejin Kananan Hafsoshin Soji (NDA) a 1986, sannan ya rike mukamai da dama a lokacin rayuwarsa, ciki har da Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da kungiyar Boko Haram a yankin Arewa-maso-Gabas.