✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Tanzania John Magufuli ya rasu

Shugaban Kasar Tanzania John Pombe Magufuli ya riga mu gidan gaskiya. Mataimakiyarsa, Samia Suluhu ce ta sanar da rasuwar Mista Magufuli a kafar yada labaran…

Shugaban Kasar Tanzania John Pombe Magufuli ya riga mu gidan gaskiya.

Mataimakiyarsa, Samia Suluhu ce ta sanar da rasuwar Mista Magufuli a kafar yada labaran kasar.

Magufuli ya rasu a ranar Laraba a wani asibiti Dar es Salaam, babban birnin kasar inda ya  yi jinya ta ciwon zuciya.

Saluhu ta ce a ranar 14 ga watan Maris ne jikin shugaban ya yi tsanani inda kuma aka kwantar da shi a asibiti.

Rahotanni sun bayyana cewa ya shafe fiye da shekara 10 yana fama da larurar.

Magufuli ya bar duniya yana da shekaru 61.