✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban ’yan sandan Japan ya yi murabus kan kashe tsohon Fira Minista

Shugaban ’yan sandan kasar Japan, Itaru Nakamura, ya ajiye aiki, saboda gazawar rundunar wajen dakile kisan tsohon Fira Ministan kasar, Shinzo Abe

Shugaban Runudnar ’Yan Sandan kasar Japan, Itaru Nakamura, ya ajiye aiki, sakamakon gazawar rundunar wajen dakile kisan tsohon fira ministan kasar, Shinzo Abe.

Nakamora ya ce rahotannin ’yan sandan yankin da aka kashe tsohon Fira ministan na nuna kura-kurai daga rundunar ya taimaka wajen nasarar kisan.

“Yayin da muka sake bincike da duba na tsanaki kan lamarin, mun ga akwai bukatar sake sabon lale a bangarenmu

“Haka ne ma ya sanya na bada takardar ajiye aikina ga Hukumar Tabbatar da Tsaron Al’umma ta kasar ranar Alhamis”, in ji Nakamura.

An dai kashe tsohon Fira Minista Shinzo Abe ne yayin da yake tattakin yakin neman zabe a ranar 8 ga watan Yuli, 2022 a yankin Nara da ke kasar.

Kisan Firamnistan Japan Abe
Kisan Firamnistan Japan Abe

Wanda ake zargi da harbin da ya kashe shi Tetsuya Yamagami, dai an kama shi nan take, kuma yana ajiye a asibitin kwakwalwa.

Sai dai kamar yadda rundunar ta bayyana, ya ce ya kashe Abe ne bisa haushin alakarsa da wani coci da ya tsana.

Kama wanda ake zargi Tetsuya Yamagami
Kama wanda ake zargi Tetsuya Yamagami

Alkaluma sun nuna Abe ne dan siyasa mafi soyuwa ga ’yan kasar, kuma Fira minista mafi dadewa kan karagar mulki.

Rahotannin sun ce a ranar da lamarin ya faru, ya ki amincewa da tafiya wajen taron da masu ba shi kariya da yawa.