✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabancin APC: Sai dai Buhari ya yi wa dan takararsa kamfe —Fayemi

Fayemi yi amai ya lashe kan dan takarar da Buhari ke goyon bayan dan takarar da Buhari ke goyon baya

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Gwamna Kayode Fayemi, ya musanta cewa gwamnonin jam’iyyarsa ta APC mai mulki sun amince da mutumin da Shugaba Buhari ke so ya zama sabon shugaban jam’iyyar.

Fayemi ya bayyana haka ne kasa da awa 24 bayan Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, ya ce gwamnonin jam’iyyar sun yi ittifaki da Buhari, sun kuma amince da wanda Buharin ya fi so ya zama shugaban jam’iyyar.

Amma a wani abu mai kama da mi’ara-koma-baya, a ranar Alhamis, Fayemi, wanda ya halarci zaman da gwamnonin APC 16, daga cikin 22 da take da su, suka yi da Buhari a ranar Laraba, ya ce bai san da maganar ba.

Da yake amasa tambaya da aka yi mishi game da batun a wani taro da Cibiyar Cigaba da Dimokuradiyya (CDD) ta shirya a ranar Alhamis, Fayemi ya ce, “Ni ma ba ni da masaniyar cewa Shugaban Kasa na da dan gaban goshi (a cikin ’yan takarar shugabancin jam’iyya), ko da yake ’yancinsa ne ya zabi dan takararsa.

“A matakin jam’iyyarmu, sai dai [shi shugaban kasa] ya fito ya yi wa dan takararsa kamfe a dandalin Eagle Square ranar Asabar, idan dan takararsa ya ci, shi ke nan, idan kuma ya sha kasa, sai ya hakura,” inji Fayemi.

A wurin taron, wakilinmu ya nemi karin haske daga gwamnan game da makomar dimokuradiyyar cikin gida a jam’iyyar APC, idan har za ta fitar da ’yan takara babu hammaya, alhali wasu sun riga sun sayi takardun tsayawa takara.

Fayemi ya kada baki ya ce, “Abin da muke son nunawa shi ne irin hadin kan da muke da shi a APC, wanda ke iya kasancewa ta fuskoki daban-daban, matukar kowane bangare ya yi na’am da abin da aka yi; Sakamakon abin da aka yin za a gani a ranar Asabar.”

Walankeluwar Fayemi

Sai dai kuma Jim kadan bayan nan ne kuma Sakataren Yada Labaran gwamnan na Jihar Ekiti, Yinka Oyebode, ya fitar da wata sanarwa cewa an yi wa kalaman mummunar fahimta.

A cewarsa, “Jama’a su sani cewa, a amsar tambayar da aka yi wa Gwamna Fayemi kan zargin shugaban kasa da kakaba wa APC shugaban jam’iyya a babban taronta mai zuwa, cewa ya yi, abin da ya fi damun shugaban kasa shi ne samun hadin kan jam’iyya.

“[Fayemi] Ba shi da masaniyar cewa akwai wani dan takarar kujerar shugaban jam’iyya da shugaban kasa yake goyon baya.

“Amma idan har shugaban kasa yana da wanda yake goyon baya, shugaban kasa mutum ne mai bin dimokura diyya, don haka masu sabanin ra’ayinsa na iya fitowa takara.

“Gwamna Fayemi shugaba ne da aka sani wanda ba ya soki-burutsu.”

Takaddamar ’yan gaban goshin Buhari

An dai jima ana takaddama, tun bayan da Buhari ya fitar wa jerin wasu mutane da yake son su samu mukami a Kwamitin Gudanarwar APC, a babban taronta da za a gudanar ranar Asabar.

Rahotonni sun sun nuna daga cikin mutanen, Buhari na so tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu ya zama shugaban jam’iyyar.

Sai dai kuma wasu gwamnoni da kusoshin jam’iyyar ba su gamsu da hakan ba, kasancewar shugaban kasar bai tuntube su ba.

Rahotanni suka nuna masu adawa da zabin Buharin na fadi-tashin ganin mutanen ba su kai labari ba.

Amma bayan wani zama da Buhari ya yi da gwamnonin jam’iyyar a ranar Laraba, Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, ya bayyana wa mane labarai cewa gwamnonin sun bayyana wa shugaban kasa amincewa da zabinsa na masu shugabannin jam’iyyar.

Ba yadda muka iya —Gwamnoni

Da yake jawabi bayan taron, Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya ce, sun yin ittifaki kan mutanen da za su rike mukaman Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Kasa.

Ya ce gwmanonin APC na goyon bayan zabin Buhari na dan takarar Shguaban Jam’iyya na Kasa.

Bagudu ya ce: “Mun yi wa shugaban kasa bayani game da rabon mukamai a yankunan siyasaa tare da nuna mishi goyon bayanmu ga zabin da ya yi na Shugaban Jam’iyya na kasa.

“Wakilai daga yankunan siyasa sun yi mishi bayani game da kokarin da suke yi domin fitar da jerin sunayen da yankunansu suka yi ittifaki a kai domin samun mukamai a Kwamitin Gudanawar Jam’iyyar na Kasa da kuma mukaman da aka ware wa kowane yanki tun da farko.

“Yawancin yankununan siyasa sun samu mukamai a Kwamitin Gudanarawar, ko da yake yawansu bai kai yawan jihohin yankunan ba.

“Duk da haka akwai kwamitocin zartarwa na yankunan siyasa, kowane yanki zai zauna ya fitar da sunayen da suka yi ittifaki.

“Gwamnan Abubakar Bello ya yi jawabi a madadin yankin Arewa ta Tsakiya; Babagana Zulum a madadin Arewa ta Gabas; Badaru Abubakar kuma a madadin Arewa ta Yamma.

“Gwamna Dave Umahi ya gabatar da jawabin maso Gabas; sai Kayode Fayemi a madadin Kudu maso Yamma; Ni kuma na yi wa Shugaban Kasa bayanin yankin Kudu maso Kudu,” a Atiku Bagudu.

Ya ce duk da haka, masu neman takarar da ba su gamsu da abin da aka yi ba suna da damar shiga a fafata da su a babban taron jam’iyyar da ke tafe ranar Asabar.

A cewarsa, jam’iyyar APC na mutunta tsarin dimokuradiyya, ba za ta tauye wa kowa hakkinsa na neman takara ba.

Da take tababtar da hakan, wata majiya mai karfi ta ce a lokacin zaman, gwamnonin, “Sun amince da matsayin Buhari a game da Sanata Abdullahi Adamu ya zama sabon shugaban jam’iyya na kasa.

“Sun kuma amince da zabinsa na sauran kujerun shugabanci a bisa tsarin karba karba a tsakanin yankunan siyasa,” inji majiyar tamu.

Shi ma wani gwamnan da wakilinmu ya zanta da shi bayan taron ya ce ko da aka dauko maganar zabin Buhari na Abdullahi Adamu a lokacin zaman, gwamnonin ba su kalubalanci zabin ba.

An cimma matsaya

Gwamnan ya kuma shaida wa wakilinmu cewa taron ya kuma daddale tare da cim ma matsaya kan mutumin da za a ba wa kujererar Sakataren Jam’iyyar APC na Kasa.

Aminiya ta gano cewa a halin yanzu, gwamnonin na kokarin kammala aikin fitar da jerin sunayen mutanen da aka yi ittifaki su zamo mambobin Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar APC na kasa.

Za su fitar ta sunayen ne daidai da tsarin karba-karba da Buhari ya amince da shi a zamansu da shi na baya.

Wakilinmu ya gano cewa Buhari ya ba wa gwamnonin wa’adin sa’a 24 su kammala aikin fitar da jerin sunayen.

Ya kuma bayar da umarnin a mayar da kudin duk ’yan takarar da suka yanki tikiti, amma ba su kai labari ba.

Buhari ya ba da wa’adi

Aminiya ta gano cewa Buhari ya ba wa gwamnonin jam’iyyar wa’adin awa 24 su mika jerin sunayen masu mukaman da suka yi ittifaki a kai.

A takardar jawabinsa ga taron da wakilinmu ya samu, Buhari ya ce wajibi ne gwamnonin su bullo da tsaftaccen hanyar tafiyar da jam’iyyar domin ta samu nasara cikin kwanciyar hankali.

“Kamar yadda na bayyana a zamanmu na ranar 22 ga watan Fabrairu, burinmu shi ne mu mika mulki ga sabuwar gwamnatin APC a matakin kasa da mafi yawancin jihohi.

“Saboda haka, kada mu kuskura mu yi kuskuren da zai sa PDP ta sake dawowa kan mulki ta mayar da kasar nan ’yar gidan jiya.

“Kamar yadda na fada a wancan lokaci, a baya mun zabi shugabanninmu ne ta hanyar samun daidaito, saboda haka ina kara kira da a sake zabar shugabanni na gaba ta wanna hanya.

“Na tabbata yin hakan ya dace da tsarin dimokuradiyya da kundin tsarin mulkin jam’iyya da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya.

“Ganin cewa sauran kwana biyu a yi babban taron, ina rokon ku da ku hada kai ku daidaita a kan mukaman jam’iyyar da suka rage cikin sa’a 24 masu zuwa, don mu samu ‘Unity List’, da za mu je taron da shi,” inji Buhari.

Ya kuma ba da umarnin a gaggauta mayar da kudaden duk masu neman takarar da ba su samu gurbi a jerin sunayen da aka yi ittifaki ba.

Yadda gwamnonin suka saduda

Idan ba a manta Aminiya ta kawo rahoto a baya cewa a ranar 24 ga watan Fabrairu Buhari ya ayyana Abdullahi Adamu a matsayin zabinsa na shugaban APC gabanin babban taronta na kasa da ke tafe ranar Asabar, 26 ga Maris, 2022.

Zabinsa na Abdullahi Adamu daga bangaren New PDP ya tayar da kura a APC, inda wasu kusoshin jam’iyyar da gwamnoni ba su ji dadi ba, bisa hujjar cewa Buhari bai nemi shawararsu a kan hakan ba.

Sai dai bayan zamansu da shi a ranar Laraba, sun mayar da wukar, sun amince da tsohon gwamnan mai shekara 76.

Mahalarta zaman sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Oshinbajo da gwamnoni 16 daga cikin 22 da jam’iyyar ke da su.

Gwamnonin da suka halarci zaman sun hada da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi sai kuma Shugaban Gwamnonin APC kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Bagudu.

Sauran su ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Filato, Simon Lalong da Gwamnan Yobe kuma Shugaban Rikon Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni.

Sauran sun mahartar zaman da aka yi gabanin babban taron jam’iyyar na ranar Asabar su ne gwamnonin jihohin Naje, Kaduna, Kogi, Ogun, Ebonyi, Imo, Jigawa, Kwara, Zamfara, Nasarawa, Osun, and da kuma Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum.

Ganawar Buhari da ’yan takara

A daren ranar Laraba, Buhari ya gana da masu neman takarar shugabancin jam’iyyar inda ya bukaci su mara wa Sanata Abdullahi Adamu baya.

A lokacin zaman, ya bayyana musu muhimmancin su amince a samu hadin kai, domin kar a samu baraka a jam’iyyar.

Mahalarta zaman su ne Sanata Abdullahi Adamu, Sanata George Akume, Sanata Umaru Tanko Al-makura, Sanata Ali Modu Sheriff; Sanata Mohammed Sani Musa, Mohammed Saidu Estu, da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Addulaziz Yari Abubakar sai kuma Saliu Mustapha.

Sauran mahalarta sun hada da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaan Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; Sakataren Gwamnati, Boss Mustapha; da Shugaban Riko da Shirya Babban Taron APC kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Wata majiya ta ce, “Buhari yana goyon bayan Sanata Abdullahi Adamu, don haka ya nemi su mara mishi baya da hadin kai domin APC ta kara karfi ta samu nasara a babban zabe.

“’Yan takarar sun amince da zabin nasa har suka yi ta raha da juna, daga baya suka yi liyafa tare da shugaban kasa, inda ya bayyana musu cewa duk mai wata matsala a cikinsu, to ya yi magana da shugaban ma’aikatansa.

“Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa sun so a ce shugaban kasa ya yi wannan tattauna da su tun kafin yanzu, amma duk da haka suna wa Sanata Abdullahi Adamu fatan alheri,” inji majiyar tamu.

Daga Sagir Kano Saleh, Ismail Mudashir, Muideen Olaniyi & Faruk Shuaibu.