✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabancin Najeriya: Dalilan da suka haifar da tarin ‘yan takara a APC

Wasunsu za su janye su mara wa sauran baya.

Muddin dai ba wani sauyi aka samu ba, ya zuwa ranar 1 ga Yunin 2022 ake sa ran Jam’iyyar APC ta bayyanar da dan takararta na Shugaban Kasa a zaben 2023.

Wannan shi ne daidai da jadawalin babban zaben 2023 kamar yadda Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta fitar a baya-bayan nan inda ta bukaci daukacin jam’iyyun da ake da su su kammala zaben fidda gwani kafin 3 ga Yuni.

A wani taron jam’iyyar da ya gudana a Otel din Transcorp Hilton da ke Abuja a ranar 20 ga Afrilu, Kwamitin Zartawa na Kasa na APC ya tsayar da ranakun 30 da 31 ga Mayu da kuma 1 ga Yunin 2022 a matsayin ranakun da jam’iyyar za ta gudanar da zaben fidda gwani na shiga takarar Shugaban Kasa.

Wannan ne ya yi dalilin masu zawarcin shugabancin kasa a karkashin tutar jam’iyyar yin tururuwa wajen sayen fom din bayyana ra’ayin shiga takarar, duk da tsawwala farashin fom din bayyana ra’ayin shiga takarar da jam’iyyar ta yi inda ta sanya fom din shugaban kasa kan miliyan N100, na gwamnoni kan miliyan N50, na sanatoci miliyan N20 sai kuma na ‘yan majalisar jihohi a kan miliyan N10, wannan bai razana ‘yan takarar yin tururuwa zuwa sayen fom din ba.

Tun bayan da jam’iyyar ta soma sayar da fom din mabukata sai karuwa suke ta yi, lamarin da har ya kai ala tilas jam’iyyar ta kara wa’adin sayar da fom din wanda da farko aka tsara sayarwa daga 6 zuwa 10 ga Mayu, amma daga bisa ta tsawaita wa’adin zuwa 12 ga Mayu.

Lamarin sayar da fom ya kai matsayin da za ka tarar da ‘yan takara kusan su 30 a lokaci guda kowannensu ya fito yana kokarin mallakar tasa fom din.

Masana harkokin siyasa na ra’ayin cewa, tun bayan da kasar nan ta koma kan turbar demokuradiyya a 1999, ba a taba gani irin haka ya faru ba.

Gabanin babban zaben 2015, ‘yan takarar da aka fafata da su a zaben fidda gwani na APC a 2004 sun hada da: Shugaba Muhammadu Buhari da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da kuma mawallafin jaridar LEADERSHIP, marigayi Sam Nda-Isaiah. Sannan a 2019 ‘yan takarar ba su kai na baya yawa ba.

‘Yan takara a wnanan karon

Kawo yanzu, wadanda suka bayyana sha’awarsu ta neman takarar Shugaban Kasa karkashin APC su ne: tosohon Gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan da Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba da Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio da tsohon Gwamnan Edo, Adams Oshiomhole da Gwamnan Kogi, Yahaya Bello da tsohon Gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun da Gwmanan Ekiti, Dokta Kayode Fayemi da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele sai kuma tsohon Gwamnan Imo, Rochas Okorocha.

Sauran sun hada da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi da Gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru da Fasto Tunde Bakare da Gwamnan Kuros Riba, Ben Ayade da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ken Nnamani da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu da Minista Kwadago da Raba Ayyuka, Chris Ngige da tsohon Gwamnan Zamfara, Sani Yarima da tsohon Ministan Yada Labarai, Ikeobasi Mokelu sai kuma kallabi a tsakani rawuna, Uju Ohanenye.

Kodayake, ‘yan Najeriya na ci gaba da nuna mamakinsu kan yawan masu zawarcin kujerar Shugaban Kasa da aka samu karkashin APC a wannan karon.

Dalilan da suka haifar da tarin ‘yan takarar Shugaban Kasa a APC

Wasu masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar APC sun bayyana dalilai da dama da suka yi musabbabin tururuwar ‘yan takarar Shugaban Kasa da aka gani a APC.

A cewar Dokta Kayode Fayemi, da yawan ‘yan takarar suna zawarcin Shugabancin Kasa ne saboda zaman lafiya da tsaron kasa su ne damuwarsu.

Kayode ya fadi haka ne sa’ilin da ya karbi bakuncin ‘yan kungiyar ‘National Prosperity Movement’ daga shiyyar Arewa maso Gabas da shiyyar Arewa maso Yamma a ofishinsa da ke Abuja. Yana mai cewa, APC na da matukar muhimmanci a zabubbukan da ke tafe.

“Kuma da ma haka ya kamata ya kasance, duba da cewa jam’iyyar ita ce mai mulkin kasa sannan tana da gwamnoni 22, mu ne jam’iyyar kasa,” in ji shi.

Shi kuwa Tinubu ya yi ra’ayin cewa, yawan ‘yan takarar shugabancin kasa da aka samu alheri ne ga dimokuradiyyar kasar nan.

Ya ce samun ‘yan takara da yawa hakan zai taimaka wajen saka kwarin gwiwa ga ‘yan takarar da kuma cire tsoron cewa samun ‘yan takara da yawa ka iya haddasa rikici a jam’iyyar bayan kammala zaben fidda gwani.

Sai dai a hirarsu da wakilinmu tsohon dan takarar Shugaban Kasa, Cif Martins Onovo ya ce, farin jinin Buhari ne ya haifar da yawan ‘yan takarar duk kuwa da tsadar fom.

Ya ce, “An yaudari wasunsu game da Buhari sannan suka dauki hakan a matsayin goya musu baya, duk kuwa da Buharin ya sha fada musu magana guda.”

Daga nan, Onovo ya bukaci hukumomi masu yaki da rashawa a kasar nan da su bincike dukkan wadanda suka lale miliya N100 suka sayi fom din bayyana ra’ayin shiga takarar a APC.

“Ina kira ga EFCC da takwarorinta da su binciki ‘yan takarar APC da suka sayi fom don bayyana ra’ayin shiga takara, saboda hakan tamkar karfafa wa rashawa ne,” in ji shi.

Kazalika, jagora a APC kuma tsohon dan takarar Shugaban Kasa, Cif Chekwas Okorie, shi ma ya ce, “A fahimtata, ina ganin abin da ya haifar da yawan ‘yan takara bangarori ne guda biyu. Na farko, saboda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bai wa ‘yan kasa ta bacin cewa za ta gudanar da zabe mai tsabta.”

Sai kuma bangare na biyu, “Tabbacin da jam’iyyun siyasa suka bai wa ‘yan takara kan cewa ba za su zauna haka kawai su fitar da dan takara ba, da wannna kowa yake gani zai samu adalcin da yake bukata,” in ji Okorie.

Haka nan, tsohon dan Majalisar Wakilai kuma dan takarar gwamna a zaben 2023 a Jihar Ribas, Bernard Mikko ya ce, “Galibin ‘yan takarar Shugaban Kasa sun shiga takara ne saboda ganin tsarin dimokuradiyya mai inganci. Suna jin cewa APC ta kimanta gaskiya bisa ga jam’iyyar hamayya wadda mutum daya kacal ke kula da ita.”

Amma a cewar Jackson Lekan Ojo, galibin ‘yan takarar sun shiga sahun takara ne “don zuba jarin da zai amfani gobensu.”

Ya kara da cewa, abin da suke kokarin yi shi ne, yin yarjejeniyar samun mukaman minista da sauran mukamai don gobensu.

“Idan ka kalli lamarin da idon basira, za ka ga cewa wasu ‘yan takarar sun sayi fom amma sun san wanda za su mara wa baya. Nan da ‘yan kwanaki wasunsu za su janye don mara wa wasu baya kuma za su cin ma yarjejeniya wajen yin hakan,” in ji Ojo.

Wata majiyarmu wadda ta hana ambaci sunanta ta shaida wa wakilanmu cewa, wasu ‘yan takarar sun shiga takara ne a matsayin wata hanya ta samun kariya da rufin asiri daga jam’iyya.

Yayin da wasu majiyoyin namu suka yi ra’ayin cewar, wasunsu sun shiga takara ne domin samar wa jam’iyyar kudaden gudanarwa a fakaice amma ba don neman cin zabe ba.

A yi waje da duk wani dan takara mai alamar tambaya a kansa – cewar Masu ruwa da tsaki

Wata majiya mai tushe a daya daga cikin hukumomin tsaron kasa, ta bayyana cewa suna sane da dukkan abin da ke gudana.

Ta ce, “Muna sane da ‘yan siyasar da ke neman mafaka. Suna shiga takara ne domin guje wa kamun hukuma saboda akwai zargin rashawa a kan wasunsu. Shi ya sa suke neman kasancewa kan mulki kowane lokaci.

“Kuma an san yadda halin ‘yan Najeriya yake, da zarar muka soma farautarsu za ka ji an fara ce-ce-ku-cen wai muna son yi wa dimokuradiyya nakasu,” in ji shi.

Wasu masana harkar siyasa da ma shugabannin jam’iyyar sun ce, zai zame wa kasar nan matsala idan aka tsayar da dan takara ko mgajin Buhari a 2023 wanda hali abin tambaya.

Wasunsu sun fada wa wakilanmu cewa idan hakan ta faru, tabbas an jefa kasa cikin wani hali mara dadi, don haka suka ce akwai bukatar jama’a su tantance su kuma darje sosai kafi su zabi dan takara a zabe mai zuwa.

Wata majiyarmu wadda aka sakaya sunanta ta ce, “‘Yan kasa idan kuka sake kuka zabi wadanda ba su wanye da EFCC ko ICPC ba, hakan zai haifar da mummunar gazawa ga kasa.

“Kamata ya yi kada kowane dan Majalisar Zartawa (FEC) ya nemi shugabancin kasa saboda sun gaza.

“Idan kana ganin kana da masaniyar dabarun da za su taimaki kasa wajen cigaba sannan ka kasa aiwatar da su duk da damar da ka samu na zama mamba a Majalisar Zartawa ta Kasa, kawai ka manta da batun son zama Shugaban Kasa. Saboda wannan ita ce Majalisa (FEC) mafi muni a tarihin Najeriya.”

Har wa yau, wani jigo a jam’iyyar ya ce, “Ina ganin so suke su dawo don su sake shashantar da ‘yan Najeriya. Galibinsu sai cewa suke za su zo don su dora daga inda Buhari ya kwana da aiki. Ke nan, hakan na nufin mu sa ran ci gaba da ganin kashe-kashen juna, fama da tsadar kayan abinci da sauransu. Don haka, nake ganin babu ko mutum guda daga ckinsu da ya cancanci zama shugaban kasar nan.”

Sai dai kuma, tsohon shugaban majalisar tuntuba na kawancen jam’iyyu (IPAC), Cif Peter Ameh, ya shaida wa wakilinmu cewa duk da dai akwai alamar tambaya game da dabi’un wasu ‘yan takarar, dokar kasa ta ba su damar shiga takara saboda ana zaton mutanen kirki ne har sai in kotu ce ta tabbatar da akasin haka a kansu.

A cewar wata majiyarmu, “Ai wannan ba shi ne karon farko da irin wannan ke faruwa ba, inda wasunsu za su janye su mara wa sauran baya ta yadda bayan kura ta lafa sai a biya su kudadensu da suka kashe wajen sayen fom da sauransu har da karin wasu damammaki a kan haka.”

‘Yan takarar da ke cikin tsaka-mai-wuya

Rahotanni na nuni da cewa wasu daga cikin ‘yan takarar wadanda ke rike da mukaman gwamnati sun shiga tsaka-mai-wuya biyo bayan umarnin da Shugaba Buhari ya bayar na duk wani mai son shiga takara ya ajiye mukaminsa don ya fuskanci takararsa.

A zaton wadanda lamarin ya shafa, za a kyale su a kan mukaman nasu ne sannan su ci gaba da harkokin takararsu, ta yadda idan ya zamana a karshe ba su kai bantensu ba, sai ungulu ta koma gidanta na tsamiya. Don haka umarnin Buhari ya kada musu hanta.

Tuni dai Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba da takwaransa na Niger Delta Affairs, Godswill Akpabio da Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu suka mika takardunsu na ajiye aiki a ranar Larabar da ta gabata.

Sauran ‘yan takarar da ke cikin tsaka-mai-wuya saboda rashin tabbas sun hada da Gwamnan CBN, Emefiele da Ministan Sufuri, Amaechi da Babban Lauyan Kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami wanda ke neman shugabancin jiharsu ta Kebbi da sauransu.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin cewa, dukkan masu rike da mukaman siyasa da suke sha’awar shiga takara su ajiye aikinsu kafin ranar 16 ga Mayun 2022