✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin da ke dasawa da Trump sun ki taya Biden murna

Lopez Obrador ya ce ba zai yi azarbabin taya murna ba sai duk wata shari'a ta kare.

Shugabanin kasashen duniya da ke dasawa da Shugaban Amurka Donald Trump, sun ki taya zababben shugaban kasa Joe Biden murnar lashe zaben Amurka, kamar yadda takwarorinsu na kasashen duniya suke ci gaba da yi.

Daga cikin shugabannin, akwai shugaban kasar Mexico, Andres Manuel Lopez Obrador, Shugaban kasa Jair Bolsonaro na Brazil da Yarima mai jiran Gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman.

Shugabannin kasar Rasha Vladimir Putin da na China Xi Jinping, na daga cikin wadanda ba su yi wa Biden fatan alheri ba.

Kafar labarai ta Aljazeera ta ruwaito cewa shugaban kasar Mexico, Andres Manuel Lopez Obrador ya ce ba zai taya Biden murna ba har sai ya yi nasarar shari’a da Trump ya shigar ta kalubalantar sakamakon zaben.

Lopez Obrador, a taron da ya yi na manema labarai, ya ce ba zai yi azarbabin taya murna ba sai duk wata shari’a mai nasaba da zaben da aka gudanar ta kare.

Ya ce kasarsa tana da kyakkyawar alaka tsakaninsa da shugaba Trump da zababben shugaba Biden, kuma shugaba Trump yana “matukar girmama mu.”

Brazil

A kakar yakin neman zabe, Shugaban kasar Brazil Bolsonaro ya yi martani a jawabin da Biden ya yi lokacin muhawararsu da shugaba Trump cewar zai kara samar da kariya ga dajin Amazon idan aka zaben shi.

Bolsonaro ya alakanta bayanin da Biden ya yi da cewar “masifa ne”,  ya kuma kira Biden da sunan da ba nasa ba, inda ya ce “Wannan abin kunya ne, Mr John Biden!”.

Rasha

Kawo yanzu shugaban kasar Rasha, Putin wanda abokin Trump ne bai ce komai ba game da zaben, sauran shugabannin da suka kame bakunansu sun hada na Isra’ila, Benjamin Netanyahu da na Indiya, Narendra Modi da kuma Shugaban kasa Rodrigo Duterte na Philippines..

Kasar Sin (China)

Matsalolin da ke tsakanin China da Amurka na iya ci gaba a karkashin zababben shugaban kasa, Biden.

Trump ya sha kiran shugaban kasar China Xi Jinping “Dan daba” ya kuma sha alwashin sai ya jagoranci kasashen duniya wajen kaurace wa da hukunta kasar china.

Kamfen din Trump kuma ya danganta abin da China ke yi wa Musulmi a kasarta a matsayin kisan kare dangi wanda hakan ka iya zama hatsari ga kasar ta Sin.

“Amurka na bukatar ta kara zafafawa a kan kasar Sin” inji Biden a cikin wata makala da ya buga kan annobar Coronavirus, da aka fara samo wa daga wani gari mai suna Wuhan, na kasar Sin.

“Babbar hanyar da za a bi shi ne a hada kai da kasashen da muke hulda da su domin fuskantar cin zarafin Dan Adam da kasar Sin ta ke yi.”

Haka nan kuma, Biden ya nemi hadin kan kasar ta Sin a fannonin da za su kawo ci gaba a Amurka kamar su dumamar yanayi da kauce wa abubuwan da za su zamo kalubale ga zaman lafiya a duniya.