✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugabannin kasashen duniya da aka yi wa kisan gilla

Akwai kuma shugabannin da aka kashe suna gadon mulki a Najeriya.

A makon jiya ne aka kashe Shugaban Kasar Haiti, Mista Jovenel Moïse a matsayin Shugaban Kasa na baya-bayan nan da aka yi wa kisan gilla yana kan karagar mulki.

Hakan ya sa Aminiya ta zakulo wasu shugabanni 20 da aka yi musu kisan gilla kamar yadda ta kalato daga shafin Wikifidiyya kamar haka:

 1. Patrice Émery Lumumba
Patrice Émery Lumumba

Lumumba na kasar Kwango dan siyasa kuma Shugaban Jam’iyyar MNC da ta yi fafutikar samun ’yancin kai, ya kasance Firayi Minista na farko a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.

Kuma shi ne ya jagoranci Jam’iyyar MNC daga 1958 zuwa ranar da aka kashe shi.

Ya rike wannan matsayi na Firayi Minista tun daga ranar 24 ga Yuni 1960 har zuwa 5 ga Satumban 1960.

An kashe shi a garin Lumunbashi birni na uku mafi girma a kasar a wasu harbehabe a ranar 17 ga Janairun 1961.

 1. John Fitzgerald Kennedy (JFK)
John Fitzgerald Kennedy

John F. Kennedy dan siyasa ne da ya zama Shugaban Amurka na 35 daga 1961 zuwa ranar da aka kashe shi a kusan karshen shekararsa ta uku a kan mulki.

An kashe shi a Lee Harbey Oswald a Dallas, Jihar Tekzas a ranar 22 ga Nuwamban, 1963.

Ya kasance Shugaban Amurka daga ranar 20 ga Janairu, 1961 zuwa 22 ga Nuwamba, 1963.

 1. Hasan Ali Mansur
Hasan Ali Mansur

Fitaccen dan siyasa ne a Iran wanda ya zama Firayi Minista daga 1964 zuwa 1965.

Yana daya daga cikin wadanda suka yi gwagwarmayar juyin-juya hali (White Rebolution) na Shah Mohammad Reza Pahlabi, inda wani dan majalisa mai suna Fadayan-e Islam ya kashe shi a ranar 26 Janairu, 1965.

Ya jagoranci kasar Iran daga ranar 13 ga Afrilun 1923 zuwa 27 ga Janairun 1965.

 1. Faisal bin Abdulaziz Al Saud
Faisal bin Abdulaziz Al Saud

Jami’in diflomasiyya ne da ya zama Sarkin Saudiyya daga ranar 7 ga Maris 1964 zuwa 26 ga Janairu, 1975.

An kashe shi a ranar 25 Maris,1975 a Riyad, Babban Birnin kasar tare da dan uwansa Faisal Ibn Musaid.

 1. François Tombalbaye
François Tombalbaye

François Tombalbaye wanda aka fi sani da N’Garta Tombalbaye malami kuma dan gwagwarmaya na Kungiyar Kwadago da ya shugabanci Jam’iyyar Chadi Progressibe Party (CPP) a 1959.

An nada Tombalbaye a matsayin Shugaban Gwamnatin Kasar bayan samun ’yancin kanta a ranar 11 ga Agusta 1960.

Ya yi mulkin kama-karya, wanda a sanadiyyar salon tafiyar da mulkin nasa ya sa sojoji suka yi masa juyin mulkin da ya yi sanadiyar mutuwarsa a ranar 13 ga Afrilun 1975 a N’Djamena.

Ya rike wannan mukami tun daga ranar 11 ga Agustan 1960 zuwa 13 ga Afrilun, 1975.

 1. Park Chung-hee
Park Chung-hee

Shugaban Kasar Koriya ta Kudu, kuma Janar na soja wanda ya Shugabanci Koriya ta Kudu daga 1963 zuwa lokacin da Kim Jae-Gyu ya kashe shi, a Seoul a ranar 26 ga Oktoban 1979.

 1. Hafizullah Amin
Hafizullah Amin

Dan siyasa a Afghanistan kuma mai fada-a-ji. An haife shi a Lardin Pagham kuma ya yi karatu a Jami’ar Kabul.

Ya fara aikin koyarwa, inda bayan ’yan shekaru yana aiki, ya tafiAmurka karo karatu.

An kashe shi a Kabul a ranar 27 ga Disamban 1979, a wani sumame mai suna Storm-333 da sojan tsohuwar Tarayya Sobiyet suka kai.

Ya kasance Shugaban Afghanistan daga ranar 14 Satumba 1979 zuwa 27 ga Disamba 1979.

 1. Ziaur Rahman
Ziaur Rahman

Hafsan Hafsoshin Sojan Bangladesh ne wanda daga bisani ya zama dan jihadi, kuma ya zama Shugaban Bangladesh daga 1977 zuwa 1981.

An kashe shi a ranar 30 ga Mayun1981 a Chittagong a yayin juyin mulkin soja.

 1. Muhammad Anwar Sadat
Muhammad Anwar Sadat

Ya kasance Shugaban Masar na uku, inda jami’an soja masu tsattsauran ra’ayi suka kashe shi a Alkahira a ranar 6 ga Oktoban 1981.

Ya rike mukamin Shugaban Kasa daga 15 ga Oktoba 1970 zuwa 6 ga Oktoban 1981.

 1. Indira Priyadarshini Gandhi
Indira Priyadarshini Gandhi

Fitacciyar ’yar siyasar Indiya wadda ta kasance jigo a Majalisar Dokokin Indiya.

Ita ce mace ta farko da ta taba zama Firayi Minista, kuma har zuwa yau, babu wata mace da ta sake kasancewa Firayi Minista a Indiya a bayanta.

Ta rike mukamin Firayi Minista daga Janairun 1966 zuwa Maris 1977 da kuma Janairun 1980 zuwa lokacin da aka kashe ta, a New Delhi a ranar 31 ga Oktoban, 1984.

Wannan ya sa ta zama Firayi Minista ta biyu mafi dadewa a kujerar bayan mahaifinta.

 1. Thomas Sankara
Thomas Sankara

Babban Hafsan Sojan Burkina Faso, mai ra’ayin kawo sauyi.

Ya rike mukamin Shugaban Kasar Burkina Faso bayan juyin mulkin da ya yi a 1983 zuwa 1987.

An kashe shi a yayin juyin mulkin da Blaise Compaore ya jagoranta a ranar 15 ga Oktoban, 1987 a Ouagadougou.

 1. Samuel Kanyon Doe
Samuel Kanyon Doe

Soja ne da ya rikide dan siyasa a Laberiya, ya kasance Shugaban Kasa na soja daga 1980 zuwa 1990, sannan daga baya ya mulki kasar a matsayin farar hula.

Ya sha azaba da wulakanci na awa 12 a hannun tsohon jagoran ’yan tawaye, Yarima Yomie.

Johnson a ranar 9 ga Satumba 1990, a Monrobiya, inda daga bisani aka kashe shi.

 • Mohamed Boudiaf
Mohamed Boudiaf

Boudiaf wanda ake kira da Si Tayeb el Watani shugaban siyasa ne na Aljeriya kuma yana daya daga cikin wadanda suka assasa juyin juya-hali a karkashin Jam’iyyar National Liberation Front (NLF).

Ya jagoranci fafutikar samun ’yancin Aljeriya (a 1954-1962).

Boudiaf ya gudu ya bar kasar bayan samun ’yancin Aljeriya, inda bai sake komawa Aljeriya ba sai bayan shekara 27.

Ya sake dawowa a 1992 don karbar mukamin Shugaban Majalisar Koli ta Kasar, inda aka kashe shi bayan wata hudu da kasancewarsa Shugaban Kasar.

An kashe shi a ranar 29 ga Yunin 1992 a garin Annaba.

Ya rike mukamin Shugaban Kasa tun daga ranar 16 ga Janairu, 1992 zuwa 29 ga Yuni, 1992.

 1. Juvénal Habyarimana
Juvénal Habyarimana

Hafsan Sojin Rwanda ne da ake yi masa lakabi da ‘Kinani’ ma’ana ba a cin nasara a kansa.

Ya Shugabanci Rwanda daga 1973 zuwa 1994, inda ya zamto mutum na biyu da ya shugabanci kasar.

Wani makami mai linzami ne ya kashe shi, a ranar 6 ga Afrilu, 1994 a Kigali.

 1. Janar Ibrahim Baré Maïnassara
Ibrahim Baré Maïnassara

Hafsan soja ne kuma jami’in diflomasiyya a Nijar wanda ya mulki kasar zuwa ranar da aka kashe shi, a lokacin juyin mulkin soja na ranar 9 ga Afrilun1999 a Yamai.

Ya mulki kasar daga ranar 27 ga Janairun 1996 zuwa 9 ga Afrilun 1999.

 1. Laurent Kabila
Laurent-Désiré Kabila

Dan kasar Kwango kuma dan siyasa ya zama Shugaban Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kwango na uku, bayan ya hambarar da Mobutu Sese Seko.

An kashe shi a ranar 16 ga Janairu, 2001, inda dansa Joseph mai shekara 29 ya gaje shi bayan kwana takwas da rasuwarsa.

Ya jagoranci kasar daga ranar 17 ga Mayun 1997 zuwa 16 ga Janairun 2001.

 1. João Bernardo “Nino” Vieira
João Bernardo “Nino” Vieira

Dan siyasar Guinea-Bissau ne da ya zama Shugaban Guinea-Bissau daga 1980 zuwa 1984; sai karo na biyu daga 1984 zuwa 1999; da kuma karo na uku daga 2005 zuwa 2009.

Sojoji sun kashe shi a ranar 2 ga Maris, 2009 a Bissau.

 1. Muammar Gaddafi
Muammar Gaddafi

Muammar wanda aka fi sani da Kanar Gaddafi, dan juyin juya-halin Libya kuma masanin siyasa.

Ya mulki Libya a matsayin Shugaban Juyin Juya Hali na Jamhuriyar Larabawan Libya daga 1969 zuwa 1977; sannan a matsayin Shugaban Brother Leader of the Great Socialist People’s Libyan Arab Jamahiriya daga 1977 zuwa 2011.

Ya rasu ne sakamakon raunin harbin bindiga da ya samu daga sojojin Kwamitin Rikon Kwarya na Kasar a wajen garin Sirte.

 1. Idriss Déby Itno
Tsohon Shugaban Kasar Chadi, Idris Deby
Tsohon Shugaban Kasar Chadi, Idris Deby

Dan siyasar kasar Chadi ne kuma hafsan soja.

Ya Shugabanci Kungiyar Patriotic Salbation Mobement,(PSM), inda daga bisani ya zama Shugaban Chadi daga 1990 zuwa rasuwarsa a ranar 20 ga Afrilun bana bayan raunin harbin bindiga da ’yan tawayen FACT suka yi masa.

Ya rasu a babban birnin Chadi na N’Djamena.

 1. Jovenel Moïse
Jovenel Moïse

Shugaban Kasar Haiti ne da aka kashe a cikin gidansa, fitaccen dan siyasa ne da ya zama Shugaban Haiti daga 2017 zuwa ranar da aka kashe shi, a makon jiya.

An kashe Moïse aka raunata matarsa Martine a wani hari a gidansu, a PétionBille, kusa da Porto-au-Prince a ranar 7 ga Yulin bana.

Tuni aka kama mutum 17 da ake zargi da hannu a hallaka Shugaban.

Bayansu akwai shugabannin da aka kashe suna gadon mulki da suka hada da Firayi Ministan Najeriya, Sa Abubakar Tafawa Balewa wanda ya yi mulki daga 1960-1966 da Shugaban Kasa na Soji Janar Aguiyi Ironsi (wata shida) da Janar Murtala Mohammed wanda ya mulki Najeriya daga Yulin 1975 zuwa Fabarairun, 1976 da sauransu da dama a sassan duniya.