Daily Trust Aminiya - Shugabannin ‘yan bindiga 4 sun mika wuya a Katsina
Subscribe

Shugabannin ‘yan bindiga 4 sun mika wuya a Katsina

Wasu karin shugabannin ’yan bindiga da suka addabi yankunan Jihar Katsina, sun tuba tare da mika makamansu ga jami’an tsaro.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, Sanusi Buba ne ya bayyana hakan, a ranar Alhamis yayin da ya gana da manema labarai a jihar.

“Babu wanda muke roko ya mika wuya. Rundunar ’Yan Sanda da sauran jami’an tsaro ba za mu kyale duk wanda yaki tuba daga addabar mutane ba.

Manyan bindigogi da ’yan bindigar suka mika ga jami’an tsaro

“Muna tabbatar wa da jama’a cewar ayyukan ’yan bindiga sun kusa zama tarihi a jihar nan, saboda jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu kan lamarin,” a cewarsa.

SP Buba, ya ce yana da yakinin cewa yadda shugabannin ’yan bindiga ke mika wuya, zai taimaka gaya wajen janyo hankali wasu ’yan bindigar da ajiye makamansu.

Kwanson harsasai

Ya ce makaman da aka sallama sun suka hada da manyan bindigogi biyu, bindiga kirar AK-49 guda daya, Ak-47 guda 23, harsashin GPMG guda 109 da kuma shanun sata guda 45.

Wasu bindigogin da ’yan bindigar suka sallama wa ’yan sanda a Jihar Katsina.
More Stories