✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sinadaran soyayya kashi (4)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga…

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.

Ga ci gaban bayani kan ilimin soyayya domin ma’aurata su fahimci wannan babban jigo na rayuwar aure kuma su dabbaka a mu’amar aure da soyayya cikin huldodinsu:

Sinadaran soyayyar auratayya: 

Ci gaba daga inda muka tsaya:

 

  1. Abota:

Sinadari na ukun soyayyar ma’aurata shi ne ya kasance akwai kyakykyawar abota tsakananin ma’aurata.

Abokantaka wata kyakykyawar zumunta ce da ke kulluwa tsakanin mutum biyu ko sama da haka wacce ke dauke da kyakykyawar sanayya da fahimtar juna da yarda da amincewa da so da kauna da kuma mutunta juna.

Kyakykyawar abokantaka na samuwa ne lokacin da mutum biyu ma’abota kauna da amintar juna, suka kasance suna yawan haduwa a kai-a-kai.

Kuma idan sun hadun suna sabunta sanayya ta hanyar tattaunawa game da kowane bangare na rayuwarsu da rayuwar mutane mafi kusanci da su, da hirar abubuwan da suka sa a gaba a wannan lokaci da tattauna abubuwan da suka sha musu kai ko wasu matsaloli da suke fama da su da taimakon juna ta kowane bangare.

Akwai kuma bai wa juna shawara da karfafa gwiwa da bayyanar da sirrukan zuciyarsu ga junansu da yin abubuwan yau da kullum tare kamar cin abinci da wasanni da ziyara da sada zumunci da hirar raha da sauransu.

A takaice dai abota wata dangantaka ce mai kyau mai dadi kuma mai cike da alheri marar iyaka.

Cikakkiyar abota ita ce wacce aka kulla saboda Allah kadai ba domin wata bukatuwa ta duniya ba; kuma sannan halayen abokan suka zo daya, hakan sai ya haifar da kyakykyawar fahimtar juna da shakuwa a tsakaninsu.

Abota mai rauni kuma ita ce wacce aka kulla a kan wata bukatuwa ta duniya kamar kudi da matsayi da daukaka ko domin son burgewa.

Abokantaka cikin rayuwar aure

Abota tana da matukar muhimmanci cikin rayuwar aure, domin abota ita ke haifar da shakuwa tsakanin ma’aurata, domin haka idan ma’aurata ba su zama abokan juna ba, zai yi wuya a samu shakuwa da sabo mai kyau tsakaninsu.

 

Fuskokin abokantakar ma’aurata

Shakikan juna: Su ne ma’auratan da suke da kammalalliya kuma cikakkiyar abota, sun fahimci kowane bangare na rayuwar junansu, tun daga shauki da halaye da abubuwan so da ki da karfi da raunin juna da sauransu.

Sannan ba su shayin gaya wa junansu dukkan sirrukansu, ba su da abokin shawara da ya wuce su yi da junansu.

Suna tsananin bege da kaunar junansu; ba abin da suke rabawa a cikin rayuwar aurensu, komai na kowa ne ba mai hana daya wani abu daga cikinsu, damuwar daya damuwarsu ce su duka, ba su ware junansu a cikin komai na harkokin rayuwarsu.

Akwai tsananin mutunta juna a tsakaninsu ta yadda ko sun samu sabani, bai sa su daina mutunta juna kuma nan da nan suke warware sabanin da ke tsakaninsu.

Aminan juna:

Ana samun irin wannan abotar tsakannin ma’aurata, ya kasance sun yarda da juna, sun amince wa juna, ba cin amana ba munafinci a tsakaninsu, sannan ba su zaluntar juna, amma duk da haka sun sanya wasu iyakoki a cikin dangantakarsu da ba su ketarewa.

Misali, ba kowane irin sirri ba ne suke iya sanar wa junansu, kamar a ce miji bai san arzikin jakar matarsa ba ita ma ba ta san zurfin aljhunsa ba; ko ya kasance abubuwan da maigida ya san ba su shafi uwargidansa ba bai sanar mata ita ma haka; ko ya kasance abokansu ko kawaye su ne abokan shawara ba ya junansu ba.

Masu fuska biyu:

Su ne wadanda a fili kamar shakikan juna suke, ta yadda ba su iyakance muhimman abubuwa daga junansu ba, suna shawartar juna, suna tattauna abubuwan da ke cikin rayuwarsu ya junansu, amma a zuci ba su aminta da juna ba, a zuci suna jin haushin juna, a zuci suna zaluntar juna.

Misali duk matar da ke fadar laifuffukan mijinta ga ’yan uwa ko kawayenta, ko mai yin asiri domin mallake mijinta, ko namijin da ke bin mata a waje da sauransu, to komai kyan dangantakarsu a zahirance, tana da babban gibi domin saboda wannan mummunan sirri da suke boyewa wanda in zai bayyana gaba daya zai share soyayyar da ke tsakaninsu.

Abokan hamayyar juna:

Akwai ma’auratan da abota ta asali ’yar kadan ce cikin dangantakarsu don haka koyaushe ba fahimtar juna ba aminci a tsakaninsu.

Sun zama kamar abokan hamayya, abin da bai kai ya kawo ba sai ya haifar da gardandanmi da jayayya a tsakaninsu.

Karin bayani

A mafi yawan auratayyar wannan zamani, an fi samun dangatakar abota ta biyu da ta uku; wato aminan juna da masu fuska biyu.

Shakikan juna da abokan hamayya kuwa su suka fi karanci.

Da son samu ne, ya fi dacewa da alfanu a ce dukkan ma’aurata su kasance shakikan juna, don cimma wannan inganci cikin rayuwar aurensu.

Domin samun hakan, sai ma’aurata su yi kyakykyawan bincike tare da yin dogon nazari domin gano ina ne dangantakar abokantakarsu take da gibi.

Sannan su dage da dukkan kokarinsu wajen ganin sun cike wannan gibi domin karuwar farin ciki da kwanciyar hankali cikin rayuwar aurensu.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.