✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Siriya ta kakkabo makami mai linzamin da Isra’ila ta harba mata

Isra’ila dai ta kai daruruwan hare-hare a kasar Siriya cikin shekara 10.

Sojojin kasar Siriya sun ce sun kakkabo wani makami mai linzami da suke zargin kasar Isra’ila ce ta harba shi a kokarin kai wa babban birnin kasar na Damascus hari ranar Litinin.

Kafafen yada labaran kasar ta Siriya sun rawaito wata majiya daga rundunar sojojin kasar na cewa kakkabowar ta kuma yi wata ’yar karamar barna, ko da yake ba ta yi karin haske a kai ba.

Isra’ila dai ta kai daruruwan hare-hare a kasar Siriya cikin shekara 10 da suka wuce, yayin da kasar ke fama da rikici.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasar Siriya (SANA) ya rawaito cewa, “Wajen misalin karfe 3:05 na safiyar Litinin, makiyanmu na kasar Isra’ila sun kai wani hari ta sama da makamai masu linzami da suke kokarin kai hari a wajen birnin Damascus.

“Dakarunmu sun mayar da martani ta hanyar kakkabo wasu daga cikinsu,” inji majiyar.

Wata cibiya da ke sa ido kan kare hakkin dan Adam a Siriya da ke zama a Birtaniya (SOHR), ta ce harin ya shafi wani bangare na wani sansanin sojojin kasar da kuma wani wurin ajiye makamai mallakin kungiyar Hezbollah, wadanda suke taimaka wa Shugaban Kasar, Bashar Al-Asad.

Cibiyar, wacce take dogaro da majiyoyi a cikin kasar ta Siriya ta kuma ce an samu asarar rayuka, ko da dai ba ta bayar da adadinsu ba.

Galibi dai Isra’ila ba ta cika yin tsokaci a kan hare-haren da take kai wa a Siriya ba, amma ta sha nanata cewa ba za ta taba barin Iran da ‘yan kanzaginta su mike kafarsu a kasar ba.

Iran dai tare da Rasha sune manyan masu taimaka wa Shugaba Bashar ta bangaren sojoji.

Harin na ranar Litinin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman dar-dar a yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da a gefe daya kuma Shugabannin kasashen duniya ke koarin taruwa don tattaunawa da kasar Iran kan yarjejeniyar makaminta na Nukiliya ta 2015, da kuma rikicin kasar Yemen.