Siyasa ce ta sa aka sallame mu daga aiki – Masu shara a Gombe | Aminiya

Siyasa ce ta sa aka sallame mu daga aiki – Masu shara a Gombe

Wasu daga cikin masu sharar yayin zanga-zangar a Gombe
Wasu daga cikin masu sharar yayin zanga-zangar a Gombe
    Rabilu Abubakar, Gombe

Fiye da mata da matasa 2,000 ne da suke aikin sharar titi a Jihar Gombe karkashin kamfanin INEX suka gudanar da zanga-zanga kan korar su daga aiki da gwamnatin Jihar ta yi.

Masu sharar dai sun ce sun shafe shekara da shekaru suna aiki karkashin kamfanin, sai a wannan karon da gwamnatin Muhammad Inuwa Yahaya ta sallame su daga aiki.

Suna dai zargin korar ta su na da alaka ne da fitowar mai kamfanin neman takarar Gwamnan Jihar a jam’yyar adawa ta PDP.

Tun a ranar 30 ga watan Maris din da ya gabata ne dai aka umarce su da kowa ya mayar da kayan shararsa ofishin gwamnati ta dakatar da kamfanin ya dauke su aikin sharar.

A yayin zanga-zangar tasu a kofar shiga Gidan Gwamnati, Aminiya ta zanta da wasu daga cikinsu inda suke ta cewa a yi musu adalci saboda su suka dade suna aikin tun ana kyamarsa.

Wata Mata Mai suna Malama Hussaina ta ce da aikin sharar take dogaro da kanta da iyalanta sai yanzu rana tsaka za a ce an kore su to ya ake so su yi da rayuwarsu.

Hussaina, ta ce, “N12,000 ake biyan mu, kuma yawan mu ya kusa 8,000, don haka a dawo da mu bakin aikinmu saboda rayuwa ta yi wahala da aikin ma lallabawa muke, ballantana kuma an kore mu” inji ta.

Ita kuwa Baba Rita fashewa ta yi da kuka inda ta ce marayun ta kawai take tunawa, wadanda ta ce yanzu an tona musu asiri.

Yunusa Adamu, wani magidanci kuwa ya ce da kudin sharar yake daukar nauyin karatunsa, sai ga shi an kore shi, hakan yake nuna masa cewa karatun zai tsaya saboda ba shi da mai biya masa kudin makaranta.

A bangaren hukumar Kula da Tsaftar Muhali ta Jihar Gombe (GOSEPA) kuwa babban manajanta, Muhammad Ahmed Kumo Soja, cewa ya yi wasu ne suka mayar da abun siyasa suka hure musu kunne.

Ya ce tun tuni kwantiragin kamfanin da gwamnatin ya kare aka sake kara masa watanni uku zuwa watan Disamba.

Ahmed Soja, ya ce masu sharar ba korar su aka yi ba, wasu kamfanoni biyun da aka sake bai wa aikin wato Cosmopolitan da Bakton Green za su ci gaba da aiki da su, ba sabbi zaba dauka ba.