✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Siyasa ce ta sa su El-Rufa’i ta da jijiyoyin wuya a kan canjin kudi – Atiku

Siyasa ce ta sa su El-Rufa’i ta da jijiyoyin wuya a kan canjin kudi - Atiku

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce siyasa ce ta sa Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da wasu sauran jiga-jigan APC yin korafi a kan batun canjin kudi.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya ce suna yin haka ne ba don kishin talaka ba, sai don saboda sun ga zabe ya taho, suna tsoron jam’iyyarsu ta fadi.

An dai yi korafe-korafe kan yadda ’yan Najeriya ke shan wahala wajen samun sabbin kudaden bayan sun shigar da akasarin tsofaffin da suke da su a bankuna.

A ranar, Juma’a, Gwamnonin Najeriya sun gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kan batun, inda daga cikinsu, muryar El-Rufa’i ta fi ta kowa amo, yana korafi kan halin da talakawa suka fada a sanadin canjin.

Sai dai a cikin wata sanarwa da Hadimin Atiku kan yada labarai, Phrank Shuaibu, ya fitar a madadinsa, ya ce akwai manufar da ta sa suke korafin.

A cewarsa, “Kalaman da muka jiyo Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i game da batun canjin kudi da wahalar da mutane ke sha abin mamaki ne ga duk wanda ya san shi.

“A daidai lokacin da ’yan Najeriya ke kokawa da wahalar canjin kudi, ba daidai ba ne a siyasantar da lamarin.

“Wannan wahalar da gangan gwamnatin APC ta kirkire ta, kuma raunin wayau ne El-Rufa’i ko wani dan APC ya alakanta PDP, ko ma ɗan takararta, Atiku Abubakar, da ita.

“Muna mamaki sosai a kan yadda wadannan ’yan APC din suka yi gum a kan wasu manufofin da suka kuntata wa ’yan Najeriya a baya,” in ji Atiku.