Siyasar bana: Ba adawa sai neman dawa | Aminiya

Siyasar bana: Ba adawa sai neman dawa

    BALARABE LADAN

Ga dukkan alamu yanzu harkar siyasa a kasar nan ta tashi daga siyasar akida ta koma harkar neman abinci inda ya sanya ’yan siyasa ke yawan canja sheka daga wannan jam’iyya zuwa wancan.

Abin takaici shi ne yadda za ka ga mutum ya tsaya a karkashin wata jam’iyya an zabe shi, amma bayan kwana biyu sai ya gudu ya bar jam’iyyar ya koma wata saboda yana ganin a sabuwar jam’iyyar da ya koma ne zai fi samun biyan bukatunsa na kashin kansa.

A kwanakin baya Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Imo, Dokta Chiji Collins, da wadansu ’yan majalisa bakwai suka canja sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC, jim kadan bayan Kotun Koli ta rushe zaben Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, wanda dan Jam’iyyar PDP ne, ta ce a rantsar da Hope Uzodinma na Jam’iyyar APC a matsayin Gwamna. Nan da nan wadannan ’yan majalisa suka watsar da jam’iyyar tasu suka rungumi wadda ta samu mulki wato Jam’iyyar APC. Tun farko an zabi Shugaban Majalisar na Imo, Dokta Collins, a karkashin Jam’iyyar APGA ne, amma don ya cimma burinsa na zama shugaban majalisa sai ya koma PDP, da ya ga ta rasa Gwamna kuma sai ya sake kwashe kayansa ya koma APC.

A Kano ma Shugaban Jam’iyyar PDP a jihar ya kwashe kayansa ya bar jam’iyyar ya koma APC jim kadan da sanarwar tabbatar da zaben Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Kotun Koli ta yi.

Haka ake ta samun yawan canja sheka da ’yan siyasa ke yi tunda kasar nan ta koma mulkin dimokuradiya a 1999, kodayake a Jamhuriya ta Daya da ta Biyu ma an samu canjin shekar, amma lamarin ya fi kamari ne a Jamhuriya ta Uku domin a baya ba a cika samun wadanda aka zaba a karkashin wata jam’iyya suna barinta suna komawa wata jam’iyya ba.

A Jamhuriya ta Biyu idan wanda aka zaba a karkashin wata jam’iyya yana so ya bar jam’iyyar ya koma wata sai dai ya ajiye mukaminsa da aka zabe shi a jam’iyyar sai ya koma wata jam’iyyar daga shi sai rigarsa, tunda an zabe shi ne albarkacin wancan jam’iyya, don haka idan zai bar ta sai ya ajiye mata kayanta ya tafi.

An yi irin haka a Jamhuriya ta Biyu lokacin da marigayi Abubakar Rimi yake Gwamnan tsohuwar Jihar Kano ( Kano da Jigawa) a karkashin Jam’iyyar PRP, amma da ya yanke shawarar komawa Jam’iyyar NPP domin tsayawa takarar Gwamna a karo na biyu, sai ya ajiye mukaminsa na Gwamna ya koma Jam’iyyar NPP  a matsayin Abubakar Rimi, ba tare da matsayinsa na Gwamna ba, wannan mukamin ya bar wa Jam’iyyar PRP tunda a karkashinta aka zabe shi ya zama Gwamna.

Amma yanzu sai aka fito da wata dabara aka ce zababben dan siyasa yana iya canja sheka daga jam’iyyar da aka zabe shi ya koma wata idan akwai baraka a jam’iyyar da aka zabe shi. Jam’iyyar PDP ce ta jaddada wannan dabarar saboda a lokacin da take  mulki wadansu mutane da aka zabe su a karkashin wasu jam’iyyu sun yi ta canja sheka zuwa Jam’iyyar PDP, don haka aka fito da wannan hujja domin kada su rasa mukamansu da aka zabe su a jam’iyyun da suka bari.

Idan an lura za a fahimci cewa yanzu an bar siyasar akida sai dai siyasar neman mukami ko kuma neman abinci, shi ya sanya ake samun matsalar canja sheka take karuwa, domin jam’iyyun ma ba su da wasu fitattun manufofi da za a iya gane su da su. Sabanin jam’iyyun da aka yi a baya wadanda kowace ke da fitattun manufofin da aka santa da su, kuma ’ya’yanta suna tsayawa tsayin-daka su kare manufofin nan, ruwa da iska ba su canja ra’ayinsu, idan wata jam’iyya ta kafa gwamnati sauran jam’iyyu suna nan a matsayin ’yan adawa, suna kara wa gwamnati kaimi domin ta yi wa jama’a aiki.

A hankali dai yanzu adawa tana ta kara raguwa tana komawa neman dawa, duk inda gwamnati take nan kowa zai raja’a saboda ya samu wani abu da zai sanya a bakin salati. Sai dai kuma ’yan siyasar da ke canja shekar nan sun kasa fahimtar yadda abubuwa ke gudana, domin da zarar sun bar jam’iyyarsu suka koma wata a mafi yawan lokuta dangwarar da su ake yi, ’yan kadan ne suke sa’a ana damawa da su. Wato dai suna yin biyu babu ke nan, babu adawa, babu dawa.