✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soja ya harbe jami’in Kwastam a Legas

Seme yanki ne na kasar Najeriya da ke iyaka da Kwatano.

Wani jami’in Hukumar Kwastam ya yi gamo da ajalinsa yayin da wani soja ya harbe shi a iyakar kan tudu ta Seme da ke Jihar Legas.

Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba da daddare.

“Da yiwuwar sojan yana cikin maye ne na barasa don babu wanda ya taba tsammanin zai yi aikata wannan barna da ba a san shi da ita ba,” a cewarsa.

Seme yanki ne na kasar Najeriya da ke iyaka da Kwatano, babban birnin Jamhuriyyar Benin.