✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Soja ya harbe karamin yaro a fadar Shehun Borno

Wani soja mai suna Bukar Mustapha Limanti da ke karkashin rundunar Operation Lafiya Dole, ya kashe wani yaro dan shekara 9 a Maiduguri, babban birnin…

Wani soja mai suna Bukar Mustapha Limanti da ke karkashin rundunar Operation Lafiya Dole, ya kashe wani yaro dan shekara 9 a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa sojan ya kashe yaron ne a ranar Talata yayin da yake harbe-harbe haka siddan a kusa da fadar Shehun Borno a Karamar Hukumar Shehuri ta Arewa da ke jihar.

Wannan lamari ya sa wasu yara biyu samun raunuka da a yanzu suke famar jinya a gadon asibiti.

Wata majiya da abin ya faru a kan idonta, ta ce dama sojan ya saba irin wannan harbe-harbe marasa dalili a cikin unguwa.

Majiyar ta ce irin haka ne ya sanya ya bude wuta kan wasu yara uku da hakan ya yi sanadiyar mutuwar daya daga cikin yaran uku, Abdu Tijjani.

Ta ce nan take sojan ya tsere yayin da aka garzaya da sauran yaran biyu zuwa asibitin ICRC da ke birnin Maiduguri inda suke samun kulawa.

“Akwai yiwuwar wannan ganganci ba zai rasa nasaba ba da kisan gillar da aka yi wa wani mutumi da bai ji ba bai gani ba a baya bayan nan” inji majiyar.

“Sojan ya fitine mu, domin kuwa a kullum yakan fita wurin aiki, amma yayin da zai dawo cikin dare yakan tayar da hankalin al’umma da bindigarsa kirar AK-47.

“Makonni biyu da suka gabata ne ya harbe wani kare da wata akuya a Shehuri. Lamarin ya tilasta wa Dagacin Shehuri ta Arewa, Digima Zubairu, ya ja kunnensa amma duk da haka ya ci gaba wannan mugun hali”, inji majiyar.

Haka nan wata majiya daga Asibitin Kwararrun na Maiduguri wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce yara biyun suna samun sauki.

Ta ce wani lamari makamacin wannan ya auku a kwanan baya yayin da wani soja ya harbe wani kurma mai sayar da goro a nan unguwar.