✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojan Gona: ’Yan sanda sun damke maharba 6 a Gombe

’Yan sanda a garin Billiri na Jihar Gombe sun yi nasarar kama wasu maharba da suka yi sojan gona a mararraban garin Kalmai na jihar.…

’Yan sanda a garin Billiri na Jihar Gombe sun yi nasarar kama wasu maharba da suka yi sojan gona a mararraban garin Kalmai na jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe,  Ishola Babatunde Babaita, ya ce an kama uku daga cikin masu sojan gonar ne sanye da rigunan soja, sauran uku kuma rigunan kungiyar maharba, dauke da bindigogin toka da kuma single barrel.

Ya ce tuni wadanda ake zargi da sojan gonar suka amsa laifin da ake zargin su da aikatawa inda suka ce wani abokinsu ne, wanda kuma soja ne a bataliya ta 151 da ke Bama a Jihar Borno amma shi dan asalin Karamar Hukumar Billiri ne a Jihar Gombe ya ba su kayan sojojin.

Daga nan sai yace yanzu haka suna ci gaba da gudanar da bincike, da zarar sun gama za su tura wadanda ake zargin zuwa kotu don yanke musu hukunci.

Sai dai kuma Kwamishinan ’Yan Sandan ya gargadi al’umma da su guji shiga miyagun kungiyoyi da aikata miyagun laifuffuka.

Ya kuma yi alkawarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma bisa yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar.