✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji 16 sun mutu a hatsarin mota a Indiya

Hatsarin ya jikkata wasu sojoji hudu.

Akalla dakarun soji 16 ne suka rasu sakamakon hatsarin mota a Arewa maso Gabashin kasar Indiya.

Hatsarin ya auku ne a ranar Juma’a yayin da motar da ke dauke sojoji ta yi hatsari a Jihar Sikkima a kan hanyarta ta zuwa kan iyakar kasar da China.

Wata sanarwa da hedikwatar sojin kasar ta fitar ta ce sojoji 16 sun kwanta dama, amma ceto wasu hudu da suka ji rauni.

Jihar Sikkim dai ta yi kaurin suna wajen rashin kyan hanyoyi, musamman babbar hanyar Himalayan da ke da iyaka da kasar Tibet.

Hanyar da ta hada iyakar China da kuma Pakistan na yawan cin rayukan sojoji a duk shekara.

A watan Agusta wasu ’yan majalisar dokokin kasar ne suka mutu a wani hatsarin mota a yankin Kashmir.