✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji 6 sun rasu bayan Boko Haram ta tarwatsa su ta kwashi makamai

Harin kungiyar na uku ke nan a kan sansanonin soji cikin wata guda a Marte

Akalla soja shida ne ake fargabar sun kwanta dama a wani sabon hari da Boko Haram ta tarwatsa sansanonin soji a yankin Tabkin Chadi a Jihar Borno.

Mayakan Boko Haram din sun yi ba-ta-kashi tare da jikkata sojoji da dama sannan suka kwashi makamai bayan da suka tarwatsa sojojin a sansanonin biyu a Karamar Hukumar Marte.

Majiyarmu ta tsaro ta ce, “daruruwan mayakan Boko Haram ne suka kawo harin; sojoji sun gwabza fada da su amma abin ya gagare su. Dakarun sun yi iya yinsu domin kare sansanonin nasu.”

Ta shaida wa Aminiya a ranar Laraba cewa zuwa lokacin wasu daga cikin sojojin da suka bazu ba su kai ga hadewa da sauran da suka koma Dikwa ba tun bayan harin.

Aminiya ta gano cewa harin da aka kai wa sansanonin sojin a garin Marye a safiyar Litinin shi ne irinsa na uku da kungiyar ta kai wa sojoji a Karamar Hukumar Marte a cikin wata daya.

Hakan kuma na faruwa ne duk da yawan sojojin da aka gairk a garin.