✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji 63 Ukraine ta kashe mana —Rasha

Ita kuwa Ukraine ta ce ta kashe sojojin na Rasha akalla 400.

Rundunar Sojin Rasha ta ce mayakanta 63 ne suka mutu a wani harin rokoki da sojojin Ukraine suka kai wani ginin da ke dauke da dakarunta a gabashin yankin Donetsk.

Ba kasafai ba ne dai Rasha ke bayar da sanarwar mutuwar dakarunta a fagen yaki ba.

A cikin wata sanarwa da ba a saba ganin irinta, Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce, an kashe sojojin kasar 63 sakamakon wani harin makami mai linzami da Ukraine ta kaddamar kan birnin Makiivka da ke gabashin Ukraine wanda Moscow ta mamaye.

Wannan ce asarar sojoji mafi girma da Rasha ta yi tun bayan barkewar yaki tsakaninta da Uktraine a ranar 24 ga watan Fabairun da ya gabata.

Rasha ta ce, an yi amfani da shu’umar na’urar cilla makaman roka da aka kera a Amurka wajen kaddamar mata da wannan farmakin, yayin da a Babban Hafsan sojin Ukraine ke cewa, dakarunsu ne suka kai harin a Makiivka.

Sai dai shi kuwa Sashen Yada Labarai na Rundunar Sojin Ukraine ya yi ikirarin cewa, kimanin sojojin Rasha 400 ne suka mutu a Makiivka sabanin 63 da aka ba da rahoto.

Ukraine ta ce ta kashe sojojin na Rasha akalla 400, bayan kuma ta kakkabo jirage marasa matuka 22 kirar Iran da sojojinta suka yi a ‘yan kwanakin nan.

Mayakan gwamnatin Shugaba Vladimir Putin dai sun kaddamar da luguden wuta a yankunan Ukraine masu yawa, ciki har da Kyiv bbabban birnin kasar, inda ta lalata wasu cibiyoyin samar da wutar lantarki a birnin.

Ukraine ta ce ta hallaka daruruwan dakarun Rasha a daren sabuwar shekara, bayan samun taimakon makaman yaki daga Amurka a daidai kuma lokacin da Rasha ke tsananta hare-hare ta sama a kasar.