✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji na shirin ko-ta-kwana bayan ISWAP ta ‘kashe’ Shekau

Rahotanni sun ce Shekau ya yi kunar bakin wake bayan ISWAP ta kama shi.

Rundunonin tsaro a Najeriya na cikin shirin ko-ta-kwana bayan bullar rahoton mutuwar shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.

Rahotanni sun ce Shekau ya mutu ne a ranar Laraba bayan ya yi kunar bakin wake lokacin da mayakan ISWAP suka ritsa shi a Dajin Sambisa, suka kuma kame dogaransa.

Bayan ya mika wuya, bangare ISWAP din ya yi zama da shi tare da bukatarsa ya sauka da mukaminsa. Ana cikin haka ne ya tayar da rigarsa kunar bakin wake ya kashe kansa da sauran mahalarta zaman.

A yammacin ranar Laraba ne rahotanni suka nuna cewa Shekau ya mutu bayan dauki ba dadi da bangarensa ya yi da mayakan ISWAP, yankin Dajin Sambisa.

Duka kungiyoyin biyu — Boko Haram da ISWAP — suna aika-aikarsu ne a kusa da yankin Tafkin Chadi.

An dade ana fitar da rahotannin kashe Shekau, amma daga baya yana fitowa ya karyata.

Wani rahoto ya ambato wani kwamandan ISWAP, Baana Duguri yana cewa bangarorin biyu sun gwabza kazamin fada a Dajin Sambisa a ranar Laraba.

Mayakan ISWAP sun jima suna hakon Shekau, wanda suke son kamawa da ransa, amma rahoton ya ce shugaban na Boko Haram ya kashe kansa ne ta hanyar tayar da gurneti domin kada su kama shi.

“Mayakan ISWAP sun yi wa shugaban na Boko Harm kawanya a yayin da fada ya kaure tsakanin bangarorin biyu.

“Da Shekau ya lura ISWAP na so ta kama shi ne a raye sai ya tayar da bom ya kashe kansa,” inji rahoton.

A halin yanzu dai hukumomin sojin Najeriya ba su yi tsokaci game da rahoton ba, amma wata majiyar tsaro ta ce Rundunar Soji da Hukumar DSS na tantance sahihancin labarin.

Tun a shekarar 2009 Shekau ya karbi jagorancin kungiyar Boko Haram bayan jami’an tsaro sun kashe shugaban kungiyar ta fakro, Mohammed Yusuf.