✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji ne ba sa so yaki da ta’addanci ya kare —Sheikh Gumi

Ya yi zargin cewa manyan sojoji na amfana shi ya sa ba sa so matsalar ta kare.

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi zargin cewa sojojin Najeriya na amfana da yaki da kasar ke yi da ta’addanci shi ya sa ba sa so matsalar ta kare.

Malamin ya yi zargin cewa zunzurutun kudaden da ake kashewa wurin yaki da ta’addanci ya sa yawancin manyan sojoji ba sa kaunar a kawo karshen matsalar.

“Sojoji ba sa taimakawa ko kadan saboda su ke cin amfana da tabarbarewar sha’anin tsaro,” inji shi a lokacin hirar da gidan talabijin na ARISE TV ya yi da shi.

Sheikh Gumi ya bayyana haka ne yayin karin haske game da ziyarar kwanan nan da yake kaiwa dazuka don yin da’awa ga ’yan bindiga su rungumi zaman lafiya su daina ta’addanci.

“A shirye ’yan bindigar suke su ajiye makamansu su koma rayuwarsu yadda suka saba a baya muddin Gwamnatin Tarayya za ta biya bukatarsu da bata taka kara ta karya ba: ta gina musu makarantu da sibitoci ta samar musu da ruwan sha.

“Suna yawan kokawa cewa sojoji na kashe mutanen da babu ruwansu. Shi ya sa suka fara daukar makamai. Ko ta ina suke samun makamai? Suka fara yin garkuwa mutane wanda shi ya haifar da wannan aikin soji.

“Amma a shirye suke su ajiye makamansu su koma rayuwa kamar sauran ’yan Najeriya idan za a gina musu makarantu da asibitoci a samar musu da ruwan sha.

“Akwai kuma zargin cewa sojoji ba sa so a kawo karshen rikicin saboda da biliyoyin Nairori da ake ba su don yakar ta’addanci. Saboda haka su ma sojojin ba sa taimakawa.

“Ina yaba wa ’yan sanda da Shugaban ’Yan Sanda musamman saboda ya taimaka mun je mun gana da waddannan mutane; amma su sojoji babu alamar za su taimaka, ba su ba da hadin kai ba; ba san dalili ba.”

Kalaman Sheikh Gumi abin takaici ne —Sojoji

Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya Mohammed Yerima, game da kalaman malamin inda ya ce abin takaici ne duk da cewa malamin na damar ya fadar ra’ayinsa.

“Abin takaici ne irin wannan magana ta fito daga malamin Musulunci mai kima. Yana da ’yancin fadin ra’ayinsa, amma abin da zan ce shi ne, rayukanmu muke sadaukarwa muna kare kasar nan kuma muna yin iya bakin kokarinmu.

“Shin shehin malamin na da hujjojin da za su tabbatar da zargin nasa? Zai iya kawo hujjojin? Wannan abin takaici ne, amma ra’ayinsa ne kuma yana da ’yancin bayyanawa,” inji Birgediya Yerima.