✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji ne suka ceto Daliban Kankara —Fadar Shugaban Kasa

Amma Gwamna Masari ya ce Miyetti-Allah ce ta shiga tsakani har aka ceto su

Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Kan Harkokin Watsa Labarai, Malam Garba Shehu ya tabbatar da cewa sojojin Najeriya ne suka ceto daliban Makarantar Sakandiren Kimiyya ta Kankara 344 a Jihar Katsina.

Ya bayyana hakan ne a cikin wani sharhi da ya wallafa ranar Lahadi mai taken, “Muhimman tsarabobi biyar daga dawowar daliban Kankara 344”.

Tun da farko dai Shalkwatar Tsaro ta Kasa ta ce dakarunta karkashin rundunar Operation Hadarin Daji ne suka ceto daliban, ikirarin da ya ci karo jawabin Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina wanda ya ce Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti-Allah ce ta taka muhimmiyar rawa wurin sasantawar da ta kai ga sako su.

Garba Shehu ya ce, “Bayan fuskantar matsin lamba daga cikin gida da waje, wadanda aka dora wa alhakin dawo da yaran gida sun jajirce matuka wajen ganin surutan mutane da cece-ku-cen da ake bai sare musu gwiwa ba ko ya dauke hankalinsu daga yin abin da ya kamata ba.

“Sun yi aiki tukuru ba tare da wani boye-boye ba har suka dawo da yaran gida cikin aminci.

“A wasu lokutan, jami’an tsaronmu ba su cika samun yabon da ya kamata su samu ba.

“Sojojin Najeriya na da manufa, sun tsara ta sannan suka aiwatar da ita yadda ya kamata ba tare da harba ko da harsashi daya ba.

“Wannan yana da matukar muhimmanci saboda idan aka rasa ko da dalibi daya daga cikinsu ne, to tabbas ran Shugaba Buhari zai baci da ma na iyayen yaran, ya kuma wargaza nasarar ceton.

“Burin Shugaban Kasa shi ne yaran su dawo a raye kuma a damka su ga iyayensu.

“A matsayinsa na uba mai tausayi, zai ji matukar bacin rai in aka ce wani daga cikinsu ya rasa ransa a yunkurin yin hakan,” inji Garba Shehu.