✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun aika ’yan Boko Haram 41 lahira a Borno

Sun ceto mata da kananan yara 60 tare da kwato manyan makamai daga mayakan kungiyar

Mayakan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannun sojojin Najeriya inda sojojin suka aika ‘yan ta’addar 41 lahira suka kuma kubutar da tsoffin mata da kananan yara 60 daga hannunsu.

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta ce dakarunta na Operation Lafiya Dole da ke Gamboru Ngala a Jihar Borno ne suka ragargaji ’yan kungiyar da safiyar ranar Litinin.

Mai magana da yawun Rundunar, Birgedia Mohammed Yerima, ya ce sojojin sun kuma kwato muggan makamai daga hannun mayakan “a ci gaba da suke yi da fatattakar mayakan Boko Haram Terrorists ISWAP a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

“Zaratan sojojin sun yi sintiri ne a yankin Gulwa da Musuri na Karamar Hukumar Gamboru Ngala , Jihar Borno.

“A Musuri, sojojin sun yi karon batta da mayakan kungiyar inda suka yi minti 45 suna musayar wuta sannan suka murkushe ’yan ta’addar suka kashe 41 daga cikinsu.

“Sun kwato manyan makamai sanna suka ceto mutu 60 da suka hada da tsoffin mata da kananan yara ’yan ta’addar suka yi garkuwa da su.

“Makaman sun hada da bindiga 20, babur daya, kekuna 6, akwatin aikin kanikanci biyu, keken dinki, baturan hada abubuwan fashewa da kwayoyin kara kuzarin jima’i da sauransu.

“Dakarunmu a shirye suke sun fatattaki ta’addanci da masu aikata shi da abin da ya rage na burbushin Boko Haram a yanki da ma kasa baki daya,” inji sanarwar.

Ta kara da cewa tuni Babban Hafsan Rundunar, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, ya jinjina wa sojojin tare da kiransu da su kara matsa kaimi.