✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun bace bayan harin Boko Haram a Marte

Boko Haram ta kwashi manyan makamai a sansanin sojin da ke garin Marte

Wasu hafsoshi da kananan sojojin Najeriya ‘sun bace’ bayan harin da Boko Haram ta kai wa sansaninsu a garin Marte na Jihar Borno.

Sojojin Bataliya ta 153 da kuma 22 Armored Brigade, da ke Marte, sun janye ne bayan harin ba-zata da kungiyar ta kai wa sansaninsu a garin.

“Sojojin sun kusa samun galaba a kan maharan sai karin ’yan kungiyar suka kai wa takwarorinsu dauki, abin da ya sa sojojin janyewa saboda karfin makaman maharan,” inji majiyarmu ta tsaro a ranar Juma’a.

Majiyar ta ce yawancin sojojin da hafsoshin sun koma sansanin sojin da ke garin Dikwa, amma zuwa lokacin ba a ga wasu daga cikinsu ba.

Ta ci gaba da cewa maharan na Boko Haram su kwashe kaya da manyan makamai daga sansanin sojin da ke Marte sannan suka cinna wawurin wuta.

Kwamandojin Birget ta 22 da Bataliya ta 153 na daga cikin sojojin da suka koma Dikwa inda Babban Kwamandan Runduna ta 7 zai gana da su a ranar Asabar, a cewar majiyar.

Sojoji sun samu dauki

Rahotanni daga baya na cewa an tura jiragen yaki domin kai wa sojojin dauki saboda barazanar harin ga mutanen garin Marte da suka koma gidajensu bayan gudun hijirar da suka yi na shekara shida.

Mukaddashih Daraktan Yada Labaran Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Birgediya Bernard Onyeuko, ya ce dakarun rundunar Operation Tura Takaibango da Sashen Sojin Sama na Rundunar Operation Lafiya Dole “sun tarwatsa motocin yaki bakwai na Boko Haram a lokacin da suke yunkurin kai wa sansanin sojin hari a Marte.

“Bayan samun rahoton harin, sai sojojin suka janye, suka yi wa mayakan kwanto a wani wuri, inda suka jira maharan suka kuma bude musu wutar da ta kai ga nasarar.

“Har yanzu sojojin na ci gaba da bin sawun maharan, kuma nan gaba za mu yi wa mutane karin bayani,” inji sanarwar ta ranar Asabar.

Ba yanzu farau ba

A ranar 1 ga watan Yunin 2020 an kai wa sojojin bataliyar makamancin wannan hari a Marte, wanda ya sa suka janye zuwa Dikwa.

Daga baya aka sake mayar da bataliyar Marte bayan an fara tura Birget din garin.

A harin na 2020, soja 18 ne suka bace kuma har yanzu babu labarinsu, duk da cewa an gano gawarwarkin uku daga cikinsu.

Zuwa lokacin kammala hada wannan rahoto dai babu cikakken bayani game da wadanda harin na ranar Juma’a ya ritsa da su.