✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun bayyana sunayen daliban Kwalejin Kaduna da aka kubutar

Daliban da aka kubutar sun hada da mata biyu da maza uku

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana sunayen dalibai biyar da ta kubutar daga cikin 39 da aka yi garkuwa da su a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka Jihar, Kaduna.

Kakakin Rundunar, Mohammed Yerima ya ce daliban sun hada da mata biyu da maza uku —Amina Yusuf, kuma Maryam Danladi Abubakar Yakubu, Francis Paul da kuma Obadiya Habakkuk.

“Ana ci gaba da duba lafiyar daliban da aka kubutar a wani asibitin sojoji a garin Kaduna.

“Babban Kwamandan Runduna ta 1, Manjo-Janar DH Ali-Keffi ya jinjina wa kokarin dakarun sannan ya bukace su da su ci gaba da kokarin ganin cewa an kubutar da daukacin wadanda aka yi garkuwa da su tare da damka su ga iyalansu,” inji shi.

Aminiya ta kawo rahoto cewa iyayen daliban ba su samu ganawa da su ba, bayan an sako su; Daga baya ne sojoji suka bayyana sunayensu.

’Yan bindiga sun kutsa kwalejin ne ranar 11 ga watan Maris da dare suka yi awon gaba da 39 daga cikinsu, yayin da sojoji suka kubutar da mutum 180 a da suka hada da dalibai da ma’aikatan kwalejin.

Bayan kwana 25 a hannu masu garkuwa da su, iyayen daliban sun ce su za su tattauna da ’yan bindigar a sako su, suna masu zargin Gwamnatin Jihar Kaduna da kasa yin katabus wajen ceto su.

Sun bayyana hakan ne bayan gawmnatin jihar ta yi barazanar hukunta duk wanda da kama yana tattaunawa da ’yan bayan ta yi watsi da bataun tattaunawa da su ko biyan su kudin fansa da suke bukata.

Masu garkuwa da daliban na neman a biya su Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansar daliban.