✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun bindige ’yan Boko Haram 22 a Borno

Sojoji sun bindige ’yan Boko Hara 22 a harin da mayaka suka kai musu a Damboa, Jihar Borno

Mayakan kungiyar Boko Haram sun An kashe wata mata mai ciki da wasu mutum bakwai a Damboa, Jihar Borno.

Shaidu sun ce maharan sun afkawa garin ne dauke da manyan bindigogi suka nufi sansanin sojin da ke garin inda sojoji suka hallaka da dama daga cikinsu.

“Ranar kasuwa ce, mutane sun tafi kasuwa, muna shirin komawa gida sai muka ji wucewar motoci kafin daga baya muka fara jin hakar harbi daga sansanin sojin.

“Sojoji sun yi awanni suna musayar wuta da su kafin ‘yan Boko Hara mdin su tsere.

“Mutanen da aka kashe din suna hanyar dawowa daga kasuwa ne suka fada a inda ake fadan.

“Cikinsu akwai mace mai juna biyu, wani almajiri da wasu mazaje guda hudu”, inji wani ganau.

Ya ce maharan sun sake taruwa suka kawo wa sojojin hari ranar Talata amma sojojin suka fatattake su.

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar Operation Lafiya Dole ba kan lamarin.

Wasu jami’an rundunar hadin gwiwar farar hula a Damboa sun tabbatar da harin, inda suka ce maharan 22 aka kashe yayin da sojoji biyar suka kwanta dama.