✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun cafke wadanda suka kai hari Cocin Owo

Manjo-Janar Lucky Irabor ya ce sojoji sun kama maharan tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro.

Hedikwatar Tsaro ta Kasa (DHQ) ta bayyana cewar ta yi nasarar cafke maharan da suka kai harin cocin Katolika da ke garin Owo a Jihar Ondo.

Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya, Manjo-Janar Lucky Irabor ne ya bayyana hakan a yayin wani taron tattaunawa da shugabannin kafafen yada labarai a hedikwatar tsaron da ke Abuja.

Manjo-Janar Irabor ya ce sojoji sun kama ababen zargin ne tare da hadin gwiwar wasu hukumomin tsaro.

A ranar Lahadi 5 ga watan Yuni ne wasu ’yan bindiga suka dira cocin St. Francis Xavier da ke garin Owo a jihar Ondo dake Kudu maso Yammacin Najeriya.

Ba su bata lokaci ba suka buda wuta kan masu ibada inda suka kashe mutum 40 tare d jikkata wasu da dama.

Wannan lamari ya tayar ya yamutsa hazo a tsakanin mabiya addinai, inda kowane bangare ke tayar da jijiyoyin wuya a kokarin kare addininsa.