✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun cafke ‘yan bindiga 5, sun kwato N20m a Katsina 

Sojojin sun kwato muggan makamai a hannun 'yan bindigar.

Dakarun ‘Operation Hadarin Daji’ sun kama wasu ’yan bindiga biyar a kauyen Daudawa da ke Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina tare da kudi Naira miliyan 19.5 a hannunsu.

Daraktan Yada Labarai rundunar, Manjo-Janar Musa Danmadami, ne ya bayyana haka ne a taron mako biyu kan ayyukan sojoji a fadin Najeriya a ranar Alhamis a Abuja.

Danmadami, ya ce an kama wadanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri, ranar 17 ga watan Nuwamba, 2022.

Ya kuma kara da cewa sojojin sun kwato wata mota da wayoyin hannu guda biyar daga hannun wadanda ake zargin.

Ya ce sojojin sun kuma kashe ‘yan bindiga uku a kauyen Yambuki da ke Karamar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2022 yayin da wasu suka gudu da raunuka.

Danmadami, ya ce sojojin sun kwato manyan bindigogi guda 91, bindig kirar AK-47 guda 2 da kuma babura guda uku.

Ya ce sun kuma kama wani da ake zargin dan bindiga ne dauke da harsashi 269 a hanya Zariya zuwa kauyen Damari a Karamar Hukumar Birnin Magaji ta Jihar Zamfara.

“Saboda haka, a tsakanin ranar 17 ga watan Nuwamba zuwa 30 ga watan Nuwamba, 2022 sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda takwas, alburusai 91 da kuma bindigogi kirar gida guda biyar.

“Sojoji sun kashe ’yan bindiga 11, sun kama 10 tare da ceto wasu mutane tara a tsawon lokacin.”

Kakakin rundunar tsaron ya ce, a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2022 rundunar sojin sama ta kai farmaki a yankin da kasurgumin dan ta’adda, Malam Illa yake a kauyen Manawa da ke Karamar Hukumar Shinkafi a Zamfara.

“Bayan harin, an tabbatar da cewa an kashe ‘yan ta’adda bakwai yayin da Mallam Illa da wasu ’yan ta’adda suka tsere da munanan raunuka,” in ji shi.

Danmadami ya ce A yankin Arewa ta Tsakiya, a ranar 28 ga watan Nuwamba, dakarun ‘Operation Safe Haven’, sun kama wani da ake zargin dan bindiga ne da bindigogi kirar AK-47 guda biyar da aka boye a cikin wata jaka a Gidan Ado da ke Karamar Hukumar Riyom a Jihar Filato.

Ya kuma ce dakarun ‘Operation Whirl Stroke’ sun kama wasu mutum biyar da ake zargin su da aikata laifuka yayin da suke sintiri a kauyukan Kwazaye, Shelena da Ukande a Karamar Hukumar Katsina-Ala a Jihar Benuwai.

Ya ce an dakarun rundunar na ci gaba da samun nasara a yakin da suke yi da masu tada zaune-tsaye a kasar nan.