✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ceto daliban FGC Yauri 9 daga hannun masu garkuwa

Sojoji sun ceto mutum tara, amma dalibi daya ya rasa ransa.

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce sojoji sun ceto malami daya da dalibai takwas daga hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da dalibai da malaman Kwalejin Tarayya ta Yauri.

Mai Bawa Gwamnan Jihar Kebbi Shawara ta Musamman Rabiu Kamba ne ya tabbatar da kubutar tasu ranar Juma’a

  1. EFCC: Mun shirya yaki da masu yi wa Bawa barazana —Matasa
  2. EFCC: Mun shirya yaki da masu yi wa Bawa barazana —Matasa

’Yan bindida da adadinsu ya kai kusan 150 a kan babura dai sun kutsa kai cikin makarantar a ranar Alhamis da misalin karfe 12:30, inda suka sace dalibai da malaman kwalejin.

Kamba, ya ce yanzu haka wadanda aka ceto din suna sansanin soji, inda ake shirye-shiryen mika su ga Gwamnatin Jihar kafin hada su da iyalansu daga bisani.

A cewarsa, “Sojoji sun kubutar da malami daya da dalibai takwas.

“Yanzu haka sun sansanin soji da ke Dirin Daji. Za a mika su ga gwamnati kafin a hada su da iyalansu,”

Aminiya ta rawaito yadda sojoji suka yi artabu da ’yan bindigar kan ceto daliban da aka yi garkuwar da su a ranar Alhamis.

Sai dai daya daga cikin daliban ya rasu yayin artabun.

Mataimakin Kwamandan Rundunar Hadin Gwiwa a shiyyar Arewa maso Yamma, Air Commodore Abubakar AbdulKadir ne ya tabbatar da hakan ga ’yan jarida ranar Juma’a.

Sojoji na ci gaba da kokarin ceto ragowar

Rundunar ’yan sandan  Jihar Kebbi ta tabbatar da cewar jami’an tsaro na ci gaba da kokarin ceto ragowar daliban da ke hannun ’yan bindigar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Nafiu Abubakar ya fitar.

Har wa yau, rundunar ’yan sandan ta musanta labarin da ake yadawa cewar da motar ’yan sandan jihar ce ’yan bindigar suka yi amfani da ita wajen kwashe daliban.

A cewar rundunar, “Muna tabbatar da cewa ba mu da bayanan motar da aka yi amfani da ita wajen garkuwa da daliban ba, amma ana ci gaba da kokarin ceto su.

“Mota fara kirar Hilux mai lamba KBSJ 29, mallakar wani Alkalin Babbar Kotun jihar Kebbi ce, wanda ’yan bindigar suka yi garkuwa da ita, kuma an sace ta ne kafin satar daliban”.