✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun dakile harin Boko Haram a Neja

Harin da aka shirya da ya zama mafi muni a Jihar Neja.

Dakarun Soji sun yi nasarar dakile wani hari da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai wa sansanin sojoji da ke Sarkin-Pawa, a hedikwatar Karamar Hukumar Munya a Jihar Neja.

Aminiya ta gano cewa, tun da farko ‘yan ta’addan sun mamaye wani yanki kusa da sansanin sojin da misalin karfe 2:23 na dare, lamarin sojoji a Sarkin-Pawa suka mayar da martani da gaggawa.

Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa, ‘yan ta’addan shiga ambaton ‘Allahu Akbar’, yayin da sojoji suka afka masu.

Salis Mohammed Sabo, kakakin gamayyar kungiyar Shiroro, ya shaida wa wakilinmu cewa, “’yan ta’adda a kokarinsu na yi wa jami’an tsaro kwanton bauna ne suka mamaye sansanin sojoji da ke Sarkin Pawa hedikwatar karamar hukumar Munya ta Jihar Neja, sai sai ba su yi nasara ba saboda sojoji na ankare.

Ya kara da cewa, “‘yan ta’addan sun zo da yawansu suna kokarin tarwatsa sansanin sojin, inda sojoji suka yi fafata da su wanda an dauki tsawon awanni biyu ana artabu har sai da sojojin suka nemi karin agaji sannan suka samu nasarar fatattakarsu.”

Ya ce kwazo da kishin da jami’an tsaro suka yi a baya-bayan nan wajen yakar ‘yan ta’adda a yankin ya dawo musu da zaman lafiya.

Aminiya ta gano cewa ba a yi asarar rayuka a bangaren sojoji ba, amma akwai alamun an kashe ‘yan ta’adda da ba a tantance adadinsu ba a yayin arangamar.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya ce harin da aka shirya zai yi matukar tayar da hankali da ba don daukar matakin gaggawa da sojoji a Sarkin-Pawa da tawagar jami’an tsaro daga Minna suka yi ba.

Gwamnan a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Cif Mary Noel-Berje, ya yaba wa sojoji da sauran jami’an tsaro bisa bajinta da suka yi wajen dakile harin da suka shirya kai wa wasu al’umma a Karamar Hukumar ta Munya da ke jihar a safiyar ranar Litinin.

“’Yan ta’addan da ake zargin ‘yan Boko Haram ne da misalin karfe 2:23 na safiyar ranar Litinin, sun yi yunkurin kai hari kan al’ummomi da wani sansanin soji da ke Sarkin-Pawa, a hedikwatar karamar hukumar Munya, amma sojoji sun fatatteku su.

“Harin da aka shirya da ya zama mafi muni, ba don sojoji sun yi azama cikin gaggawa ba.

“Ba a samu asarar rayuka daga bangaren sojojin ba yayin an kashe ‘yan ta’adda da dama kana wasu daga cikinsu sun tsere da raunukan harbin bindiga,” a cewarsa.

Ya ce gwamnatin Jihar Neja ta jinjina wa kokarin da sojoji suka yi da sauran jami’an tsaro a yankin da ke fama da rashin tsaro a jihar.

“Hakika gwamnati da al’ummar Jihar Neja suna da kwarin guiwar yadda jami’an tsaronmu a koda yaushe suke kai dauki duk lokacin da aka yi kokarin kai hari.”

Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin jihar da ta tarayya na kawo karshen ta’addanci da ‘yan fashin daji a jihar.

Ya yi kira da a ci gaba da ba da hadin kai da addu’o’i daga ‘yan kasa domin bai wa gwamnati da jami’an tsaro damar samun nasara a ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda da suke yi.