✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun dakile sabon harin Boko Haram a Damboa

Cikin minti 30 da kawo harin sojoji suna fatattaki mayakan na kungiyar Boko Haram

Dakarun sojin Najeriya sun dakile wani hari da mayakan Boko Haram suka nemi kurdawa cikin garin Damboa a Jihar Borno.

Sojoji sun fatattaki maharan ne da misalin karfe 6.35 na safiyar Juma’a, bayan mayakan sun yi ta luguden wuta ta kowace kusurwa a garin.

Majiyarmu ta tsaro ta ce, “Ina tabbatar muku cewa mayakan Boko Haram sun kawo hari da sanyin safiyar yau, amma ba su yi nasara ba, nan take sojojin da aka girke a Damboa suka fatattake su.”

Majiyar ta ce ba a yi minti 30 da kawo harin ba sojoji suka ce da wa Allah Ya hada su ba in ba da mayakan na Boko Haram ba, su kuma suka ranta a na kare.