✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun dakile yunkurin juyin mulki a Sudan

Sai dai gwamnatin kasar ta ce yanzu iko ya dawo hannunta.

Hukumomi a kasar Sudan sun tabbatar da yunkurin juyin mulki da wasu ayarin sojoji suka yi yunkurin aiwatarwa amma bai yi nasara ba a ranar Talata.

Gidan talabijin na kasar ya yi kira ga jama’ar kasar su tashi tsaye wajen nuna adawa da yunkurin juyin mulkin, amma bai bayar da cikakken bayani ba.

“Yanzu komai ya dawo karkashin ikonmu, yunkurin bai yi nasara ba,” inji Mohamed Al Faki Suleiman, mamba a gwamnatin sojin mulkin kasar kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Daga bisani kuma gidan talabijin din kasar ya ci gaba da sanya wakokin kishin kasa.

Wata majiya daga cikin sojojin ta ce wasu sojoji da ba a san adadinsu ba ne suka yi yunkurin mamaye gine-ginen gwamnati da dama a yunkurinsu na yin juyin mulki amma aka dakile su.

Jami’in, wanda bai amince a ambaci sunansa ba saboda ba shi da hurumin yin magana da ’yan jarida ya ce tuni aka kama sojoji da dama, ciki har da wasu manya daga cikin sojojin.

Sai dai bai yi cikakken bayani ba, amma ya ce nan ba da jimawa ba sojojin za su fitar da sanarwa a kai.

Ababen hawa dai sun ci gaba da kaiwa da komowa kamar yadda suka saba, ciki har da a kusa da hedkwatar sojojin kasar, inda yawan zanga-zanga ta kai ga hambarar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar Al-Bashir a wani juyin mulkin cikin gida.

Tun bayan kifar da gwamnatin ne dai kasar take shirye-shiryen komawa mulkin Dimkoradiyya gaba daya.

Yanzu haka dai gwamnatin rikon kwaryar kasar ta sojoji da fararen hula ce take jan ragamar kasar har zuwa lokacin da za a dawo da cikikkiyar gwamnatin Dimkoradiyya.

Sai dai bambance-bambancen siyasa da matsin tattalin arziki da gwamnatin ta gada daga ta Al-Bashir na kawo mata tarnaki daga shirin mika mulkin.