✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun gano matatu 14 da ke tace mai ba bisa ka’ida ba a Neja Delta

An gano ana amfani da su ne wajen tace man da aka sata.

Hedkwatar Tsaro ta Kasa ta ce dakarunta sun gano wasu matatu guda 14 makare da man sata wanda suke tacewa ba bisa ka’ida ba a sassa daban-daban na yankin Neja Delta.

Mai rikon mukamin Daraktan Sashen Yada Labarai na hedkwatar, Birgediya Janar Bernard Onyeuko, wanda ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis, y ace dakarun da ke karkashin rundunar Operation Delta Safe ne suka sami nasarar a cikin mako biyu.

Daraktan na bayani ne yayin da yake karin haske kan ayyukan da sojoji suka yi a fadin kasa tsakanin tara zuwa 23 ga watan Disamba.

Ya ce matatun, wadanda haramtattu ne, suna da tukwanen dafa mai guda 13, na sanyaya shi guda 15, ramin adana man guda 15, sai ramuka biyar da kuma manyan tankuna guda 33.

Ya kuma ce a sakamakon aikin, sun sami nasarar kwato lita 896,500 da leda 70 na tataccen man a yankin.

Birgediya Janar Bernard ya kuma ce an gano kimanin lita 11,000 na kalanzir din da aka tace ba bisa ka’ida ba da kuma lita 689,000 na danyen mai.

“Bugu da kari, mun gano fayif-fayif din tunkuda mai har guda 28,manyan motocin tanka guda uku da kuma kwalekwalen katako guda 12 da ake amfani da su wajen satar man.

“Tuni mun damka duk wadanda muke zargi da kuma kayan da muka kama ga hukumomin tsaron da suka dace don daukar mataki,” inji shi.

Ya ce an kai hare-haren ne a yankunaa da kauyuka daban-daban da ke gabar ruwa a Ikwere da Fatakwal da Emouha da Ahoada ta Gabas da kuma Karamar Hukumar Bonny ta Jihar Ribas.

Sauran sun hada da kauyuka a Kananan Hukumomin Warri ta Kudu da ta Kudu maso Yamma a Jihar Delta da kuma Burutu a Jihar Bayelsa.