✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kama makamai a fadar sarakunan Binuwai

Sojoji sun tsare basarake, sun kona fadar takwaransa bayan bankado makaman

Jami’an soji sun kama tarin makamai da aka boye a fadar wasu sarakuna a Karamar Hukumar Ukum ta Jihar Binuwai.

Shaidu sun ce bayan bankado makaman a fadar Hakimi Cif Utambe Adzer  ke da wuya, sai sojojin Rundunar Operation Whirl Stroke suka cukuikuye shi.

Samamen sojojin daga ranar Juma’a da dare zuwa safiyar Asabar, ya kuma gano makamai a Fadar Hakimin Lumbuv, Cif Teran Kwaghbo.

Mazauna a yankin sun shaida wa Aminiya cewa Cif Teran Kwaghbo, ya yi batar dabo kafin sojojin su damke shi, amma sun kona fadar tashi.

Yin layar zanar Cif Teran ke da wuya sojoji suka banka wa fadarsa da ke Karamar Hukumar ta Ukum.

Wani shaida ya tabbatar wa Aminiya cewa sojojin sun bincike fadar basaraken na farko ranar Juma’a da dare, inda suka gano makaman.

Ya ce a lokacin ne sojojin suka tisa keyar basaraken, zuwa safiyar Asabar kuma sojoin suka yi wa fadar daya basaraken dirar mikiya.

A baya-bayan nan hare-haren kabilanci da ’yan bindiga sun dade suna addabar yankin Sankera na Jihar Binuwai, wanda ya hada Kananan Hukumomin Ukum, Logo, da Katsina.

Ana zargin cewa yawanin haren-haren, yaran tsohon shugaban ’yan ta’abban yankin, Terwase Akwaza, wanda aka fi sani da Gana, suke kaiwa.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin Rundunar Sojin, Birgediya Clement Apere, amma abin ya gagara.