✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kama ‘yan bindiga 21, sun ceto mutum shida a Katsina

A ci gaba da ragargazar ‘yan bindigar da su ke yi, rundunar tsaro ta ‘Operation Hadarin Daji’ ta ceto mutum shida da aka yi garkuwa…

A ci gaba da ragargazar ‘yan bindigar da su ke yi, rundunar tsaro ta ‘Operation Hadarin Daji’ ta ceto mutum shida da aka yi garkuwa da su tare da masu taimakon ‘yan bindiga har su 21 a jihar Katsina.

Shugaban Yada Labarai na Rundunar Tsaron Najeriya, Manjo Janar John Enenche ya ce sojoji sun kai harin ne a dazukan Gobirawa da Bawa-Daji na Karamar Hukumar Batsarin jihar ta Katsina, bayan samun bayanan sirri kan ‘yan bindigar a ranar 20 ga watan Yuni.

Manjo Janar Enenche ya ce dakarun sun iske dandazon ‘yan bindigar kuma suka cika karfi suka tarwatsa su da makaman da suka dara na ‘yan bindigar wadanda ya ce sun fantsama cikin dazuka.

Daga bisani dakarun sun gano cewa harin ya ragargaza ‘yan bindigar matuka bayan sun rika ganin jini na malala a hanyoyin da ‘yan bindigar suka bi don tserewa.

Ya ce jiragen yakin kojoji sun lalata sansanonin ‘yan bindigar akalla guda biyar tare da kwato bindigogi hudu, babura biyar sai kuma kakin sojoji guda biyu da sauran kayayyaki.

Manjo Janar Enenche ya ce a ranar ta 20 ga watan Yuni ce kuma sojoji suka kai hare-hare a kauyukan Biyaka, Randa, Ruma, Garin Inu, Shekewa, Gurbin Tsauni da kuma Garin Buda duk a karamar hukumar ta Batsari, inda suka samu nasarar kwato bindiga mai jigida da kuma wayoyin salula guda hudu.