✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kara kashe masu zanga-zanga 7 a Sudan

Kawo yanzu masu zanga-zanga 71 ke nan aka kashe tun bayan juyin mulkin wda Janar Abdel Fattah al-Burhan ya jagoranta.

Sojojin kasar Sudan sun bude wuta tare da kashe karin mutum bakwai daga cikin masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojojin suka yi.

Kawo yanzu masu zanga-zanga mutum 71 ke nan sojoji suka kashe tun bayan juyin mulkin da Janar Abdel Fattah al-Burhan ya jagoranta a ranar 25 ga watan Oktoban 2021 a kasar ta Sudan.

Jami’an lafiya sun ce a ranar Litinin sojoji sun bude wuta kan masu zanga-zanga suka kashe mutum hudu daga cikinsu.

Bayanin nasu na zuwa ne bayan Babbar Majalisar Likitocin Sudan ta sanar cewa sojoji sun kashe wasu masu zanga-zanga uku a Khartoum, baban birnin kasar.

Kasar Sudan dai ta kasance cikin rudani tun bayan juyin mulkin na 2021, wanda daga bisani sojojin suka janye, suka dawo da Fira Minista Abdalla Hamdok kan kujerarsa.

Sai dai masu zanga-zangar sun yi watsi da dawo da shugabancin Hamdok da kuma duk wata yarjejeniya da sojoji suke da hannu wajen gudanar da gwamnatin kasar.

Daga baya dai Fira Minista Hamdok ya yi murabus daga mukaminsa, a yayin masu zanga-zanga a sassan kasar suka ci gaba da dagewa cewa dole sai sojoji sun tsame kansu cakokam daga harkokin siyasa.

Tun bayan hambarar da gwamnatin Shugaban Umar Hassan Al Bashir a wata tarzoma da ta barke saboda tsadar burodi a Sudan, kasar take ta tangal-tangal.