✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun yi wa gidan gwamnatin Imo kawanya

Soji dauke da manyan makamai sun yi wa Gidan Gwamnatin Jihar Imo kawanya

Jami’an sojoji dauke da manyan makamai sun yi wa Gidan Gwamnatin Jihar Imo kawanya domin hana masu zanga-zangar #EndSARS shiga ofishin gwamnan jihar.

Sojojin dai sun isa fadar gwamnatin ne da sanyin safiya inda suka tsaya a muhimman wurare, a daidai lokacin da dokar hana fita da aka sanya a jihar ta fara aiki.

Mutane da dama a jihar sun yi ta fitowa da safe saboda rashin sanin cewa Gwamna Hope Uzodinma ya ayyana dokar a jawabin da ya yi wa al’ummar jihar da yammacin ranar Talata.

Kazalika, yara da dama sun fita zuwa makaranta kafin daga bisani hukumomi su kora su gida.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a ranar Laraba wasu matasa sun yi yunkurin kona wani caji ofis a yankin Ihiagwa amma daga bisani rokon da jami’an da ke ciki suka yi ta yi ya tserar da shi.

To sai da ya zuwa rana, mazauna garin da dama sun yi ta kokarin komawa gida domin kauce wa yiwuwar barkewar rikici, yayin da ‘yan sanda suka yi kokarin tirsasa su bin dokar ta hana fita.