✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe gomman ’yan ta’adda a Neja

Babu tabbas ko shi ma Aminu Duniya ya mutu a harin.

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ce dakarunta sun samu nasarar kashe gomman ’yan bindiga a Jihar Neja.

Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet ne ya tabbatar da hakan ranar Lahadi a Abuja.

Sanawar da rundunar ta fitar ta ce a ranakun karshen makon ne ta kai harin a kan ’yan bindiga da suke mubaya’a ga wani Kwamandan kungiyar Boko Haram, Aminu Duniya.

A cewar Gabkwet, an kai wa ’yan ta’addan hari ne a lokacin da Duniya ke jagorantar wani taro da mayakan kungiyar a garin Kurebe na Karamar Hukumar Shiroro.

“Yayin da sojojin kasa suka toshe hanyoyin yankin, jirgin sojin sama ya bude wuta a inda ’yan ta’addan suke, wanda an tabbatar da mutuwar ’yan ta’addan masu yawa.

“Sai dai babu tabbas ko shi ma Aminu Duniya ya mutu a harin,” a cewar sanarwar.

An kai harin ne sa’o’i kadan bayan rundunar ta ce ta kashe wasu gomman ’yan bindiga a yankin Galbi na Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.