✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe kwamandojin Boko Haram

Mayakan da suka mika wuya sun ce son kudi da neman iko ne suka sa su shiga Boko Haram

Dakarun rundunar Operation Lafiya Dole ta Najeriya sun ragargaji wasu kwamandojin kunigyar ISWAP wadda aka fi sani da Boko Haram da ke kokarin shiga Dajin Sambisa da ke kasar daga Jamhuriyar Kamaru.

Sojojin sun karkashe mayakan kungiyar su shida bayan samun bayanan sirrin a kan kai-komonsu a yankin dajin Sambisa a ranar 17 ga watan Yuli.

“Tatsar layin sadarwar kungiyar da muka yi ya tabbatar da cewa an kashe babban kwamandan Boko Haram mai suna Sayinna da wasu mayaka”, inji kakakin rundunar, Manjo Janar John Enenche.

“Mun gano wasikar da aka rubuta wa Abu Fatima (babban kwamandan kungiyar) da wasu takardun sirri da kuma wasu kayayyaki”, inji shi.

Babban hafsan ya ce, “Sauran mayakan da sojoji suka halala sun hada da wasu kwamandojin Boko Haram biyu da ke boyewa a jejin Sambisa.

Manjo Janar Johhn Enenche ya ce sojoji sun kuma kwace bindigogi da albarusai da ababen hawa da na’urorin sadarwa daga mayakan da suka halaka.

Ya ce ko a farkon wantan Yuli sojoji sun kashe manyan kwamandojin kungiyar guda takwas da suka jagoranci wani hari a kan babban sansanin Sojin Kasa da ke Damasak, jihar Borno.

Wasu daga cikin shugabannin kungiyar da ya ce an halaka sun hada da: Tumbun Dabino – Ba Issoufou, Tumbun Bororo – Amir Batam, Tumbun Jaki – Almustapha, Tumbun Bagaruwa – Modou Kollo, Dogon Tchoukou – Issah, Tumbun Rakke – Mustapha Woulama, Tumbun Dila – Boukar Kowa, da kuma Tumbun Mita – Abou Aisha.

Ya ce nasarorin sun sa “Mayaka da dama mika wuya ga sojoji suka kuma bayyana cewa son kudi da neman iko ne suka kai su ga shiga kungiyar ba wata akida ba”.