✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe matasa 5 a hanyar daurin aure a Taraba

Da ganin baburan matasan sai sojojin suka bude musu wuta ba kakkautawa

Wasu matasa biyar sun gamu da ajalinsu a hannun sojoji a Jihar Taraba inda sojojin suka bude musu wuta bisa kuskure da tsakar dare.

Matasan na hanyarsu ta dawowa daga daurin aure abokinsu ne suka yi karo da sojojin da ke sintiri a kauyen Bassa da ke Karamar Hukumar Ardo-Kola.

Sojojin sun yi zaton cewa matasan da suka yi goyo a kan babura da misalin karfe 12 masu garkuwa da mutane ne, nan take kuma suka bude mutu wuta, suka bindige biyar daga cikinsu.

Daya daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya ya ce a hanayrsu da dawowa daga wani daurin auren wani abokinsu a kauyen Garin-Baka ne suka yi gamo da sojojin a kauyen Bassa.

Umar wanda dalibi ne a Jami’ar Jihar Taraba ya ce daga ganin jerin gwanon baburansu, sai sojojin sun bude musu wuta.

Ya ce shi kanshi ya tsira ne bayan sun yi yanke a cikin daji, amma abokinsa Habu da ya goyo shi a babur an harbe shi kuma nan take ya rasu.

Biyu daga cikin wadanda aka kashe din dalibai ne a Jami’ar Jihar Taraba, daya kuma dalibi ne a Kwalejin Aikin Gona da ke Jalingo.

Kisan gilla ne —Iyaye

Iyayen matasan da suka je daukar gawarwakin a dakin ajiyar gawa na Asibitin Tarayya da Jalingo sun zargi sojoji da yi wa ’ya’yansu kisan gilla, domin ’ya’yan nasu ba masu laifi ba ne.

Mahaifin biyu daga cikin mamatan, Ballo Aliyu Jen ya zargi sojojin da kashe masa ’ya’ya da gangan kuma daga kurkusa.

“Muna bukatar adalci, dole a kama sojojin da laifi saboda babu wani laifin da ’ya’yanmu suka aikata,” inji shi.

Daliban sun hada da Abdulkadin Bello, Tukur Bello, Philip Yakubu, Habu Yarima da kuma Ya’u Misa.

Aminiya ta nemi samun karin bayani daga kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, ASP Leha Reform, amma hakan ba ta samu ba.