✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram 32 a Borno

’Yan ta’addan da suka razana suka tsere sun yi watsi da dukiyoyinsu da makamansu.

Sojoji sun samu nasarar kashe ’yan ta’adda 32 ciki har da wani babban kwamandan Boko Haram, Abu Iliya.

Dakarun Operation Hadin Kai tare da Rundunar Hadin Gwiwa ta CJTF sun samu nasarar ce a wani samame da suka kai a sansanonin ‘yan ta’addan a Karamar Hukumar Konduga ta Jihar Borno.

Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro da tayar da kayar baya a yankin Tafkin Chadi ne ya bayyana hakan a wannan Lahadin.

A cewar Makama, sojojin sun samu wannan nasarar ce bayan wani sintiri da jami’an leken asiri suka yi a wasu maboyar Boko Haram a kauyukan Kayamari, Habasha da Yuwe na Karamar Hukumar ta Konduga.

Kazalika, wata majiya ta bayyana cewa sojojin sun gwabza da ’yan ta’addan a yayin da suke sintirin yaki da ta’addanci a Yuwe.

Majiyar ta ce wasu daga cikin ’yan ta’addan da suka razana suka tsere sun yi watsi da dukiyoyinsu da makamansu.

Wakilinmu ya ruwaito cewa sojojin sun kuma lalata kekuna 50 da aka kwato a maboyar ’yan ta’addan.

Manjo Janar Ibrahim Ali, sabon kwamandan rundunar Operation Hadin Kai shiyyar Arewa maso Gabas, ya sha alwashin ci gaba da kokarin kawo karshen yaki da masu tayar da kayar baya.

Manjo Janar Ibrahim Ali ya ce dole ne kowa ya tashi tsaye domin ganin an kawo karshen ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Konduga dai na da tazarar kilomita 35 daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno inda ake samun rahotanni da dama na ayyukan masu tayar da kayar baya a makonnin da suka gabata.