✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe mayakan ISWAP sama da 100 a Tafkin Chadi

Dakarun sun yi nasarar kashe da dama tare da kwace miyagun makamai

Dakarun soji da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya, Nijar da kuma Kamaru, sun kashe mayakan ISWAP fiye da 100 a yankin Tafkin Chadi.

Rahotanni sun ce daga cikin adadin har da manyan kwamandoji 10 yayin wasu hare-hare ta sama da ta kasa a yankin.

Kakakin rundunar sojin hadin gwiwar ta kasa da kasa, Kanar Mohammed Dole ne ya bayyana hakan ranar Litinin.

Ya ce dakarunsu da suka kutsa cikin yankunan da masu tayar da kayar bayan ke iko da su a yankin Tafkin Chadi, sun samu nasarar kwace makamai masu yawan gaske, da kayayyakin abinci da kuma miyagun kwayoyi.

Kanar Dole ya kara da cewa sojoji 18 ne suka samu raunuka yayin artabun da mayakan na ISWAP wanda suka binne bama-bamai a gefen hanya.

Sai dai bai yi karin haske kan ko an samu salwantar rayuka daga bangaren dakarun nasu ba a sakamakon gwabzawar da suka yi da mayakan ja ISWAP.

Dole dai bai bayar da lokacin aikin ba ko adadin sojojin da aka kashe, amma ya ce sojoji 18 ne suka jikkata sakamakon wasu bama-bamai da aka binne a kan hanya.

Mayakan Boko Haram da kungiyar da ta balle daga yankin yammacin Afirka (ISWAP) sun shafe fiye da shekara 10 suna fafatawa da sojojin Najeriya a wani rikici da ya barke a jihohin da ke makwabtaka da kasar.

Hare-haren Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya ya yi sanadin mutuwar dubban mutane yayin da miliyoyin mutane kuma ke tserewa daga mahallansu zuwa sansanin ’yan gudun hijira.